'Yan sanda sun gano kamfanin kera bindigu a Kudu

'Yan sanda sun gano kamfanin kera bindigu a Kudu

Jami'an 'yan sanda da ke runduna ta musamman na Eagle-Net da ke jihar Delta sun samu gagarumin nasara cikin yaki da masu aikata miyagun ayyuka da su keyi bayan gano wani kamfanin kera bindigogi a garin Oleh a karamar hukumar Isoko ta Kudu da ke jihar.

'Yan sandan sun damke wani Isaac Uroleh mai shekaru 55 da wani Goodluck Ivivie mai shekaru 53 a harabar kamfanin a yayin da suka kai samame.

Abubuwan da suka gano sun hada da bindigu 23, harsasai guda 15 da wasu samfurin harsasan guda 4 da kuma kayayakin da ake amfani da su wajen kera bindiga masu wuyan samu.

'Yan sanda sun bankado kamfanin kera bindigu a Kudu
'Yan sanda sun bankado kamfanin kera bindigu a Kudu
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Masifar da ta fi Boko Haram na nan tafe a kasar nan - Sarki Sanusi

Binciken da Daily Sun ta gudanar ya nuna cewa addreshin gidan kere bindigun, No 5 Etoo Stree, Oleh a karamar hukumar Isoko ta Kudu waje na mutane suka saba hada-hada musamman baki daga wasu jihohin da ke zuwa sayan bindiga.

Wata majiya ta bayyana cewa galibin wadanda ke zuwa sayan bindigun matasa ne masu shekaru daga 18 zuwa 28 kuma an gano mafi yawancinsu daliban makarantun gaba da sakandire ne da ke cikin kungiyoyin asiri.

Yan sandan sun kai samamen ne misalin karfe 2 na rana a ranar Talata 13 ga watan Nuwamban 2018 wadda hakan ya kawo karshen wannan mummunan sana'an da aka kwashe shekaru ana yi.

Da ya ke tabattar da afkuwar lamarin, Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Andrew Aniamaka ya ce mutanen da aka kama suna tsare a hedkwatan hukumar da ke Asaba kuma za a cigaba da bincike domin gano dukkan masu hannu cikin lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel