Shugaban kasa Buhari ya gana da Shugabannun Kamfanin LADOL a Aso Villa

Shugaban kasa Buhari ya gana da Shugabannun Kamfanin LADOL a Aso Villa

Mun ji cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da aniyar Gwamnatin sa na habaka tattalin arzikin ta hanyar jawo masu hannun jari cikin kasar tare da samawa dinbin matasa ayyukan yi.

Shugaban kasa Buhari ya gana da Shugabannun Kamfanin LADOL a Aso Villa
Shugaban kasa Buhari yace tsare-tsaren da ya kawo su na aiki a Najeriya
Asali: Facebook

Shugaba Buhari yayi jawabi a fadar Shugaban kasa jiya, a lokacin da ya gana da Shugaban wani Kamfani na LADOL da kuma manyan Ma’aikatan sa. Buhari ya yabawa Kamfanin na yin amfanin da damar da Gwamnatin sa ta bada.

Mai magana da yawun bakin Shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana cewa Buhari ya jinjinawa Kamfanin na LADOL na shiga cikin harkar kasuwancin man fetur. Shugaban ya kuma ji dadin yadda Kamfanin ya dauki Matasa aiki.

KU KARANTA: Atiku, Saraki da Kwankwaso sun yi wani zama domin doke Buhari

Babbar Darektar wannan Kamfani, Dr. Amy Jadesimi ta bayyanawa Shugaba Buhari irin manufar su tare da yabawa Gwamnatin nan na ba kowa damar shiga harkar man fetur. A baya dai Gwamnati ta kebe wasu ‘Yan Mowa ne a harkar.

Cif Oladipo Jadesimi, wanda shi ne ya mallaki Kamfanin na DALOL yace Gwamnatin Shugaba Buhari ta basu damar zuba Dala Biliyan a Najeriya tare da daukar Matasa fiye da 50, 000 aiki a dalilin yakar cin hanci da rashawa a Kasar.

Shugaban Muhammadu Buhari ya nuna cewa yana da matukar sha’awar ganin Kamfanoni su na zuba kudi a bangaren man fetur da kuma horas da Matasa su samu sana’ar da ba na hannun Gwamnati ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel