Hukumar shirya jarabawar NECO ta sauya ranar da za’a fara zana jarabawar

Hukumar shirya jarabawar NECO ta sauya ranar da za’a fara zana jarabawar

Hukumar shirya jarabawar kammala karatun sakandari a Najeriya, NECO, ta dage ranar da ta sanya domin fara zana jarabawar zuwa ranar 19 ga watan Nuwambar shekarar 2018, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito mukaddashin shugaban NECO, Abubakar Gana ne ya sanar da haka a ranar Laraba, inda yace da fari sun sanya ranar fara zana jarabawar a 15 ga watan Nuwamba, amma a sakamako sauye sauye da aka samu sun daga shi zuwa 19 ga wata.

KU KARANTA: Hadimar Buhari ta zayyana sunayen manyan mutane 51 da aka halaka a mulkin PDP, karanta

Hukumar shirya jarabawar NECO ta sauya ranar da za’a fara zana jarabawar
Jarabawar
Asali: Depositphotos

A dalilin haka ne shugaban NECO ya kira ga duk daliban da suka yi rajistan zana jarabawar dasu sauke sabon jadawalin jarabawar a shafin hukumar na yanar gizo ‘www.mynecoexams.com’.

Daga karshe Gana ya bayyana damuwarsa da halin da wannan mataki ka iya jefa daliban da suka kammala shirin fara jarabawar, don haka ya nemi afuwansu.

Jarabawan NECO na daga cikin manyan jarabawa guda uku da ake bukatar duk wani dalibin da yake ajin karshe a makarantun sakandari ya zana kafin ya kammala karatunsa a wannan mataki, daga cikin jarabawar akwai WAEC, jarabawar kammala sakandari ta yankin Afirka ta kudu.

Sauran sun hada da JAMB, jarabawar shiga jami’a da manyan makarantu, jarabawar NABTEB, wanda daliban aji shida na makarantun sakandari na kimiyya da koyan sana’o’in hannu suke zanawa kafin su kammala karatunsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel