Majalisa Sakkwato ta amince da murabus din mataimakin gwamnan jihar

Majalisa Sakkwato ta amince da murabus din mataimakin gwamnan jihar

Majalisar jihar Sakkwato ta amince da murabus din mataimakin gwamnan jihar, Ahmad Aliyu. Aliyu ya yi murabus ne a safiyar yau Laraba 13 ga watan Nuwamban 2018.

Aliyu da mai gidansa Gwamna Aminu Tambuwal sun lashe zabe ne a karkashin tutar jam'iyyar APC amma daga baya Tambuwal ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a watan Augustan 2018.

Aliyu ya ki ficewa daga jam'iyyar APC wadda hakan yasa daga baya ya samu tikitin takarar gwamna a karkashin jam'iyyar ta APC a babban zaben 2019.

Majalisa Sakkwato ta amince da murabus din mataimakin gwamnan jihar
Majalisa Sakkwato ta amince da murabus din mataimakin gwamnan jihar
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gumi ya fadi hukuncin da ya dace a rika yiwa masu fyade

Aliyu ya sanar da murabus dinsa ne a wata wasika da ya aike wa Majalisar Jihar a ranar 13 ga watan Nuwamban 2018 wadda mataimakin Kakakin Majalisar, Abubakar Magaji ya karanto a ranar Laraba.

A cikin wasikar, tsohon mataimakin gwamnan ya mika godiyarsa ga Allah bisa damar da ya bashi na yiwa jihar hidima sannan ya bayyana cewa ya ajiye aikinsa daga ranar 13 ga watan Nuwamban 2018.

Ya kuma mika godiyarsa ga Gwamna Aminu Tambuwal, 'yan Majalisar Jihar da dukkan al'ummar jihar Sakkwato bisa goyon bayan da suka bashi yayin gudanar da ayyukansa.

Tuni dai gwamnatin jihar ta fara neman wanda zai maye gurbin Ahmad.

Cikin wadanda ake sanya ran za su dare kan kujerar mataimakin gwamnan sun hada da Kwamishinan ruwa na jihar, Hon. Umar Nature, Hon. Sagir Attahiru Bafarawa da kuma Hon. Aliyu Mohammed.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164