Babban dalilin da yasa mataimakin gwamna jahar Sakkwato ya yi murabus

Babban dalilin da yasa mataimakin gwamna jahar Sakkwato ya yi murabus

Mataimakin gwamnan jahar Sakkwato, Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto ya yi murabus daga mukaminsa a ranar Talata 12 ga watan Nuwamba sakamakon sabani daya kunno kai tsakaninsa da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

Sai dai wata majiya ta karkashin kasa mai sika ta bayyana cewar mataimakin gwamna Ahmed Aliyu ya jefar da kwallon da mangwaro ne don ya huta da kuda bayan samun labaran akwai yiwuwar majalisar dokokin jahar ta tumbukeshi.

KU KARANTA: Sarki Muhammadu Sunusi ya nemi gwamnati ta fara biyan Malaman Musulunci albashi

“Ka san nan bada jimawa ba gwamnan da mataimakinsa zasu fara gogoriyon neman mulki, musamman a zaben mukamin kujerar gwamnan jahar a 2019, kuma hakan zai iya kai ga tsige mataimakin gwamnan daga mukaminsa, ina ganin matakin daya dauka ya yi daidai.” Inji shi.

Haka zalika majiyar tace tuni tsohon mataimakin gwamnan ya mika ma majalisar dokokin jahar takardar ajiye aiki, amma majalisar bata karanta takardar a zamanta na ranar Talata ba, shima wani dan majalisar ya tabbatar da samun wasikar.

Dan majalisan yace ba wai mataimakin gwamnan ya yi murabus saboda yana samun matsala da maigidansa bane, sa’annan ba wai ya ajiye aikin saboda an tilasta masa bane, ko kum don za’a tsige shi ba.

Amma duk kokarin da majiyarmu ta yi ta jin ta bakin kaakakin mataimakin gwamna Ahmed Aliyu, Abubakar Bawa, don tabbatar da dalilinsa na yin murabus yaci tura, tunda baya amsa waya kuma bai maido da amsar tambayar da aka yi masa ta sakon kar ta kwana ba.

A yanzu haka shi mataimakin gwamnan shine dan takarar gwamnan jahar Sakkwato a karkashin inuwar jam’iyyar APC, ma’ana zai fafata da maigidansa, gwamna mai ci, Aminu Waziri Tambuwal a zaben 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng