Gumi yace bai ga dalilin da zai sa Gwamna El-Rufai ya dauki mataimakiya Musulma ba

Gumi yace bai ga dalilin da zai sa Gwamna El-Rufai ya dauki mataimakiya Musulma ba

Fitaccen malamin addinin islama dake jahar Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya bayyana cewa jahar Kaduna ba ta kai matsayin da za ayi gwamna Musulmi, mataimakin gwamna na Musulmi ba idan aka duba al’adun jama’an jahar.

Gumi ya yi wannan magana ne dangane da zabin gwamnan jahar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai, wanda ya zabi wata mata musulma Hajiya Hadiza Balarabe a matsayin mataimakiyarsa yayin da zaben 2019 ke karatowa inda mataimakinsa Bala Bantex zai koma neman mukamin Sanata.

KU KARANTA: APC da wasu jam’iyyu 7 sun hada karfi da karfe don yi ma PDP taron dangi a zaben jahar Kwara

Jaridar Premium times ta ruwaito Gumi ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ta yi da shi a ranar Talata 13 ga watan Nuwamba, inda yace irin haka ne ka iya janyo tashin hankali a tsakanin al’ummar jahar.

Majiyar Legit.com ta ruwaito Gumi yace kamata yayi a janyo kabilu da addinai daban daban dake jahar Kaduna, ba wai a yankesu ba a sha’anin mulki, ya kara da cewa akwai bukatar kananan kabilu su samu wakilci a mukaman gwamnatin jaha, idan aka yi la’akari da yawansu.

“Kowa ya san siyasace kawai, kowa ya san haka, abinda nake nufi shine ka duba lokaci, yanayi, al’ada, da sauransu kafin ka dauki irin wannan mataki, a ganina lokaci bai yi ba da za’a fara samun haka, musamman a yanzu da rikicin kabilanci ya janyo asarar rayukan mutane.

“Don haka ban ga dalilin daukan wannan mataki ba jim kadan bayan irin wannan rikici ba, musamman irin matakin da zai kara janyo rarrabuwan kawuna a tsakanin jama’a ba. ina magana ne akan yan asalin jahar Kaduna, janyosu ake yi a jiki ba wai ka waresu ba.” Inji shi.

Gumi bai tsaya nan ba har sai da yace: “Sun ce wai an samu irin haka a jahar Filato da wasu jihohi, haka ne, amma kamata yayi mu kuma mu nuna musu cewa muna da tsari.

"Ba wai a Kaduna kadai ba, muna neman kwatar ma Musulman Benuwe, Filato da Nassarawa hakkokinsu a siyasa. Idan ta kama su samu mataimakin gwamna a jihohin nan, sai a basu” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel