Buhari ya ci abinci tare da shugabannnin duniya a kasar Faransa, Hotuna
A yau, Lahadi, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci wani taron cin abinci da aka shirya domin karrama shugabannin kasashen duniya da ke halartar wani taro na kasa da kasa a kan inganta zaman lafiya a kasar Faransa.
Shugaba Buhari ya samu damar ganawa da babban sakataren majalisar dinkin duniya (MDD), Antonio Guterres, da ragowar shugabannin kasashe da dama domin tattauna yadda za a hada karfi da karfe domin samun zaman lafiya a kowanne bangare na duniya.
A daren jiya, Asabar, ne jaridar Legit.ng ta kawo ma ku labarin cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa kasar Faransa domin halartar taron kasa da kasa a kan zaman lafiya da za a yi, a karo na farko, tsakanin ranakun 11 da 13 ga watan Disamba, 2018.
A sanarwar da ta fito daga fadar shugaban kasa a jiya, Juma'a, Femi Adesina, kakakin shugaba Buhari ya sanar da cewar Buhari zai sadu da babban sakataren Majalisar dinkin duniya da ragowar shugabannin duniya domin tattauna gudunmawar da kowa zai iya bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.
Kazalika shugaba Buhari zai halarci taron cin abinci da shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya shiryawa ragowar bakin da su ka halarci taron. Buhari, bayan ya sauka a kasar Faransa Gwamnatin kasar Faransa da hadin gwuiwar wasu kungiyoyi ne su ka shirya taron domin tattaunawa a kan muhimman batutuwan da zasu tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
DUBA WANNAN: Sabon harin Boko Haram a Maiduguri: An kashe mutum, an kone gidaje
Kafin ya dawo Abuja, shugaba Buhari zai gana tare da tattaunawa da 'yan Najeriya mazauna kasar ta Faransa.
Daga cikin 'yan rakiyar shugaba Buhari akwai; gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, gwamna Willie Obiano na jihar Anambra, da gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti. Ragowar 'yan rakiyar su ne; ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; ministan shari'a, Abubakar Malami; mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Babagana Monguno; da babban darektan hukumar leken asiri ta kasa, Ahmed Abubakar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng