Da duminsa: Masoya Mama Taraba 5000 sun koma APC

Da duminsa: Masoya Mama Taraba 5000 sun koma APC

Dan takarar gwamnan APC a jihar Taraba, Sani Abubakar, ya karbi magoya bayan Mama Taraba, tsohuwar ministar jam'iyyar da ta koma jam'iyyar UDP domin yin takarar gwamna, fiye da 5000.

Masu canja shekar sun hada da shugabannin jam'iyyar APC na kananan hukumomi da mazabu da su ka bi tsohuwar ministar zuwa jam'iyyar UDP.

Da yake karbar ma su canja shekar a yau Asabar, Abubakar, ya bayyana cewar sakin sunayen 'yan takara da hukumar zabe (INEC) ta yi ya kawo maslaha a matsalolin da jam'iyyar APC ke fama da su a jihar.

Ya shaidawa wa dukkan 'yan jam'iyyar APC a jihar Taraba cewar yanzu lokaci ne na bukatar hadin kai domin tabbatar da nasarar APC a zaben shekarar 2019.

Da duminsa: Masoya Mama Taraba 5000 sun koma APC

Masoya Mama Taraba 5000 sun koma APC
Source: Depositphotos

Dan takarar ya sanar da cewar zai yanzu zai mayar da hankali wajen sulhunta fusatattun 'ya'yan jam'iyyar APC.

"Na ji dadi da ku ka gane kuskuren ku a kan lokaci kuma yanke shawarar dawowa cikin gidanku, jam'iyyar APC.

DUBA WANNAN: Babban malamin Kirista a Najeriya ya lissafan dalilan da ya sa musulunci ya fi Kiristanci

"Ina mai sanar da ku cewar akwai babban kalubale a gaban mu, kar mu bari rudun jam'iyyar UDP ya yaudare mu.

"Ina mai tabbatar ma ku da cewar akwai 'yan takara da dama da su ka nuna sha'awar goya mana baya domin ceton jihar Taraba jama'ar ta," a cewar Abubakar.

Jagoran ma su canja shekar, Adamu Kata, tsohon sakataren jam'iyyar UDP, ya ce sun canja sheka ne domin son ceto jihar Taraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel