An gargadi jama'a kan cin wake dake warin kalanzir ko fiya-fiya

An gargadi jama'a kan cin wake dake warin kalanzir ko fiya-fiya

- An gargadi 'yan Najeriya dasu guji amfani da wake kafin su tafasa shi

- 'Yan kasuwa na amfani da "Sniper" don gudun lalacewar shi

- Ya kamata a dunga wanke duk wani nau'in kayan abinci don gujewa fadawa hatsari

An gargadi jama'a kan cin wake dake warin kalanzir ko fiya-fiya

An gargadi jama'a kan cin wake dake warin kalanzir ko fiya-fiya
Source: Depositphotos

CPC ta gargadi 'yan Najeriya dasu guji amfani da wake ba tare da sun tafasa shi ba.

Daraktan hukumar Babatunde Irukera yace ya zama dole suyi wannan kira duba da wata sanarwa da aka aiko musu na cewa ana amfani da "Sniper" a cikin wake don gudun yayi kwari.

Ya kara da cewa ya kamata mutane su dunga wanke duk wani nau'in abinci kafin su dafashi don gujewa faruwar matsala.

Ya kara da cewar sun tabbatar da cewa ana amfani da Sniper musamman a kasuwanni don hana waken ya lalace da kuma bashi kariya saboda kwari.

Sannan ya kara da bayyana hatsarin dake cikin amfani da Sniper a cikin kayan abinci.

DUBA WANNAN: Yawan masu mutuwa a Najeriya daga shan sigari ya kai 7m

Sniper dai shine piya piya, mai hana kwari cin abinci ajiyayye, sai dai kuma yana da babbar illa sosai ga jikin dan adam, kuma ya zuwa yanzu, babu wanda zai iya cewa suwa ke wannan aika-aika, bayan da aka sami wake da yawa suna warin maganin.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel