Mayakan Boko Haram sun kai ma matafiya harin kwantan bauna, sun kashe da dama

Mayakan Boko Haram sun kai ma matafiya harin kwantan bauna, sun kashe da dama

Wasu mayakan Boko Haram sun kai ma ayarin matafiya harin kwantan bauna yayin da suke kan babban hanyar jahar Borno, inda suka halaka mutane da dama, tare da jikkata wasu dayawa, kamar yadda jaridar Daily Trust at ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito wani sojan sa kai na rundunar Civilian JTF ne ya bayyana haka, inda yace yan ta’addan sun kai farmakin ne a ranar Alhamis 8 ga watan Nuwamba da misalin karfe 5:30 na dare a tsakanin garin Longomani da Musini dake cikin karamar hukumar Ngala.

KU KARANTA; Manyan shuwagabannin kungiyar Izala sun jaddada goyon bayansu ga Ganduje

Mayakan na Boko Haram sun bude ma ayarin motocin matafiyan wuta ne, daga nan bayan sun kashe na kashewa sai suka banka motocin wuta, daga ciki harda motocin dake dauke da kayayyakin abinci.

“Sun bindige fasinjoji da dama, wasu fasinjojin kuma sun tsere cikin daji domin samun mafaka tare da tsira da rayukansu, daga cikin wadanda suka tsere har da dakarun Sojojin Najeriya.

“Akalla sun kona motoci biyar, daga ciki har da manyan motoci guda biyu dake dauke da kayan abinci, kananan motoci kirar Golf guda biyu da wata motar Pijo.” Inji shi.

A wani labarin kuma wasu mayakan Boko Haram sun kai mugun samame a yankin kudancin jahar Borno a daren Talata, inda suka yi sacen sacen kayayyakin abinci, daga bisani suka banka ma duk wani gida dake kauyen wuta, suka tsere.

Legit.com ta ruwaito cewar a sakamakon wannan harin mazauna kauyen na Kala dake kusa da karamar hukumar Damboa sun yi batan dabo, ko sama ko kasa an nemesu an rasa har bayan tafiyan yan ta’addan.

Wani shaidan gani da ido ya tabbatar ma majiyarmu cewa da misalin karfe 9 na daren Talata yan ta’addan suka kunno kai cikin kauyen, inda suka bude ma mazauna kauyen wuta irin na mai kan uwa da wabi, wanda yayi sanadiyyar mutuwar wasu, wasu kuma suka jikkata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel