Tsohon Soja ya halaka mutane 12 a harbin mai kan wuya a gidan giya

Tsohon Soja ya halaka mutane 12 a harbin mai kan wuya a gidan giya

Wani tsohon Sojan rundunar Sojan ruwa ta kasar Amurka ya bindige mutane goma sha biyu a wani gidan giya dake jahar California, daga cikinsu har da wani jami’in Dansanda, kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.com da misalin karfe 11:30 na dare ne wannan tsohon Soja ya bude ma mashaya giyan wutan a unguwar Thousand Oaks dake da nisan kimanin kilomita 65 daga birnin Los Angeles.

KU KARANTA: Bani da masaniyar cewa gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa muka je fashi ba – Barawo

Tsohon Soja ya halaka mutane 12 a harbin mai kan wuya a gidan giya
Dan bindiga
Asali: Depositphotos

Rahotanni sun bayanna cewa akwai akalla mutane dari biyu a cikin mashayar giyan mai suna Borderline Bar and Grill, musamman duba da cewa harin ya faru ne a daidai lokacin da wasu dalibai suka yi tururuwa suna gasar rawa.

Sai dai majiyar ta ruwaito sunan wannan dan bindiga a matsayin Ian David Long, kuma shekarunsa ashirin da takwas a rayuwa (28), amma wasu rahotanni sun tabbatar da cewa a farkon shekararnan jami’an kiwon lafiya na hukumar yansanda suka wankeshi daga zargin samun tabin hankali.

An mikashi ga jami’an hukumar ne saboda wasu halayya daya fara nunawa a gida, wadanda suka tsorata da ire iren abubuwan da yake yi a gidan, daga nan suka tafi dashi zuwa cibiyar kula da masu tabin hankali.

Rundunar Yansandan California ta bayyana cewa da karfin tuwo David ya afka cikin mashayar bayan ya bindige mai tsaron wurin, inda ya jefa wata bam mai tayar da hayaki a cikin dakin rawan, daga nan ne ya fa bude musu wuta irin na mai kan uwa da wabi.

Kaakaki rundunar Yanandan jahar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace David ya yi amfani ne da wata bindiga kirar Glock .45 calibre, wanda ko a jahar California ma an haramta amfani da ita.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng