Jihohi goma dake samun matsalar network yayin yin waya, katsewar layi - NCC

Jihohi goma dake samun matsalar network yayin yin waya, katsewar layi - NCC

- Ana samun karin matsalar Network a kan layukan sadarwa

- Hakkin mai layi ne ya sami layi mai kyau yayin waya

- NCC na sanya idanu kan kamfunna masu wahal da kwastoma

An rage yawan yin wayoyi a kasar nan, ko menene dalili? Leka rahoton
An rage yawan yin wayoyi a kasar nan, ko menene dalili? Leka rahoton
Asali: UGC

A sabon rahoton NCC na wata-wata, an sami tsaiko da gurbacewar layukan sadarwa na wayar salula a hannun lkamfanin Glo da 9-mobile, tsohuwar Etisalat, inda a jihohi goma aka sami layi na katsewa kwastomomi ana tsaka da waya.

Jihohin sun hada da Adamawa, Bauchi, Bayelsa, Borno, Cross River, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, Kastina, Kebbi, Niger, Plateau, Taraba, Yobe, Zamfara, da Sokoto, kuma NCC din tace tana bin kadin yadda za'a kare jama'a daga asarar kudadensu na waya.

DUBA WANNAN: 'In an fara fada a wurin zabe ku watse'

A rahoton na wata-wata, an kuma gano yadda kamfunnan kan dami mutane da talla ko ma saya musu wasu abubuwan da basu saya ba.

Jihohi irin su Bayelsa, Delta, Edo, Ekiti, Katsina, Kebbi, Kwara, Ondo, Osun, Oyo, Sokoto, da Yobe abin yafi shafa.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel