Karku shiga in aka fara rigima a wurin zabe, NYSC ta gargadi masu bautar kasa

Karku shiga in aka fara rigima a wurin zabe, NYSC ta gargadi masu bautar kasa

- Anyi kira ga yan bautar kasa da karsu hana yan siyasa diban kayan zabe

- Ku taimaka ku kai musu mota don gudun faruwar matsala

- Kune manyan gobe karku bata rayuwar ku akan yan siyasa

Karku shiga in aka fara rigima a wurin zabe, NYSC ta gargadi masu bautar kasa

Karku shiga in aka fara rigima a wurin zabe, NYSC ta gargadi masu bautar kasa
Source: Original

Brigadier General na NYSC Suleiman Kazaure yayi kira ga yan bautar kasa wadanda za'a dauka don gudanar da zaben shekara ta 2019 da karsu hana yan siyasar diban kayan zabe.

Da yake zantawa dasu jiya a Camp din su dake Darkingari jihar Kebbi, Kazaure yace "idan yan siyasa suka nemi daukar kayan zabe karkuyi musu dasu ku taimaka musu ma ta hanyar kai musu kayan bakin mota Dan gujewa matsala".

DUBA WANNAN: Yadda DSS tayi da Oshiomhole kan zargin cin hanci a APC

Sannan ya hanesu da karbar na goro a yayin gudanar da zaben.

Kazaure wanda ya wakilci Mrs Victoria Ango yace " kune manyan gobe to karku bari yan siyasa su bata muku rayuwa".

Sannan yace hukumar zabe ta INEC zata horar da yan bautar kasar yanda zasu gudanar da aikin su a yayin gudanar da zaben.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel