Kotu ta kama tsohon ‘Dan wasa Ronaldinho da ‘Dan uwan sa da laifi
Mun ji cewa wata Kotu a Kasar Brazil ta tasa tsohon ‘Dan wasan Duniya Ronadinho a gaba inda har ta bada umarni a karbe takardun sa na fasfo bayan an same shi da laifin yin gini a inda bai dace ba.
Labari ya zo mana daga Kasar waje cewa wata karamar Kotu a Garin Rio Grande do Sulta da ke cikin Kasar Brazil ta hukunta Ronaldinho bayan ya gaza biyan wani tara da aka ci sa da wani ‘Dan uwan sa na Dala Miliyan 2.
Kotu ta kama tsohon ‘Dan wasan na Barcelona da kuma ‘Dan uwan sa ne da laifin gina gida a wurin da bai halatta ba. Hakan ya sa aka ci tarar ‘Dan kwallon kudi har kusan Dala Miliyan 2 wanda a yanzu ya gagara bibiya.
KU KARANTA: Kasar Amurka na kokarin ganin an yi zabe cikin kwanciyar hankali a Najeriya
Kotun ta Majisatare ta bada umarni a karbe fasfon tsohon Tauraron na Duniya a dalilin kin biyan taran da aka ci sa bayan samun sa da laifin da aka yi. Da aka bincika cikin asusun ‘Dan wasan dai ba a samu komai ba sai fam £5.
Bayan Lauyoyi sun rasa yadda za su yi da 'Dan wasan ne su ka nemi a karbe takardun sa na fasfo domin a hana sa barin kasar. Duk da haka dai har yanzu Ronaldinho yana yawon sa a kasashen Duniya ya kuma ki zuwa gaban Kotu.
Karamar Kotun ta kuma kama wani babban kamfani mai suna Reno Constructions and Incorporations Ltd da laifin yin gini a inda ake kiwon kifi ba tare da amincewar Hukuma ba wanda hakan laifi ne babba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng