Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu manyan Limamai guda 4 a Delta

Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu manyan Limamai guda 4 a Delta

Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da wasu manyan limaman cocin katolika guda hudu a garin Umutu/Abraka cikin karamar hukumar Ethiope ta gabsa ta jahar Delta, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta bayyana cewa yan bindigan sun sace limamn cocin ne a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Ekpoma na jahar Edo, inda suka yi kwamba a lokacin da suka fito daga garin Warri na jahar Delta.

KU KARANTA: Dubun wata mata dake satar jarirai a Asibiti ya cika A Kaduna

Fastocin na cikin kwamban motoci guda hudu ne yayin da yan bindigan suka kai musu harin kwantan bauna a ranar Talata 6 ga watan Nuwamba, don haka basu iya tare motocin duka ba, sai dai suka tare motoci biyu wadanda suke dauke da fastocin guda hudu.

Da majiyarmu ta tuntubi kwamishinan Yansandan jahar, Muhammadu Mustafa, shima ya tabbatar da faruwar lamarin, amma yace zasu gudanar da cikakken bincike don kama yan bindigan da suka aikata laifin.

A wani labarin kuma, wasu gungun yan bindiga sun yi awon gaba da wasu manyan fastoci mata guda hudu da wasu mutane guda biyu a unguwar Railway dake garin Agbor ta jahar Delta.

Da fari sai da yan bindigan suka fara harbin motar da fastocin suke ciki, wanda hakan yayi sanadiyyar jikkata mutane biyu a cikin motar, daga nan ne suka yi awon gaba da mutane guda shida daga ciki.

Kwamishinan Yansandan jahar Muhammadu Mustapha ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace lamarin ya faru ne a ranar 28 ga Oktoba, kuma fastocin sun fito ne daga cocin Martha and Mary dake cikin karamar hukumar Ika ta kudu.

Daga karshe kwamishina Mustapha yace jami’an Yansanda suna iya bakin kokarinsu wajen ceto Fastocin tare da kama duk masu hannu cikin satar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel