Za'a biya diyyar Khashoggi daga lalitar gwamnati a Saudiyya

Za'a biya diyyar Khashoggi daga lalitar gwamnati a Saudiyya

- Kasar Saudia zata biya diyyar dan jarida daya mutu

- Ance za'a kuma maidowa iyalanshi gawarshi

- An nemi shi an rasa kafin daga bisani a gano kashe shi aka yi

Za'a biya diyyar Khashoggi daga lalitar gwamnati a Saudiyya
Za'a biya diyyar Khashoggi daga lalitar gwamnati a Saudiyya
Asali: Depositphotos

Kasar Saudia ta bayyana cewa zata biya diyyar dan jarida daya rasa ransa a lokacin da yake ziyartar ofishin jakadancin kasarsa a Turkiyya.

A yayin wata tattaunawa da CNN tayi da iyalan mamacin Salah da Abdallah sunce a dawo musu da gawar mahaifin su domin a binneshi a kasar sa wato Medina dake kasar Saudi Arabia, sannan sunce sun yadda da sarki Salman akan kokarin binciko wadanda sukayi wannan aika aika don a hukuntasu.

Wannan nuna rashin tausayi na kashe Kashoggi ya taba shugaban cin sarkin na Saudia.

DUBA WANNAN: 'Yan shia na kokarin zare ma soji ido da lasar takobi

Haspel wanda ya ziyarci kasar ta Turkey a watan daya gabata dangane da bincike akan mutuwar Kashoggi yace an bada umarnin kashe shi ne daga wasu manya na kasar Saudi.

A ranar Litinin ne gwamnatin Turkey ta bayyana cewa an tura wasu mutane 11 a 11 ga watan October wanda yayi dadai da kwanaki 9 da bacewar Kashoggi bayan ya shiga ofishin jakadancin Saudia don amsar takaddar izinin auren Cengiz wadda ta kasance yar kasar Turkey.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel