Sarkin Gombe ya gina wani katafaren Asibiti don amfanin talakawansa

Sarkin Gombe ya gina wani katafaren Asibiti don amfanin talakawansa

Mai martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar na Uku ya yi wani babban hubbasa wajen cigaban fannin kiwon lafiya a jahar Gombe, inda ya gina ma talakawansa wani katafaren Asibiti, kamar yadda wani ma’abocin Facebook, Haji Shehu ya bayyana.

Majiyar Legit.com ta ruwaito Sarki Abubakar ya gina wannan asibiti ne a unguwar Bolari dake cikin garin Gombe, inda a yanzu haka an kammala aikin ginin, sai dia kayan aiki kawai ake jira isowarsu don asibitin ya fara aiki.

KU KARANTA: An bayyana wasu abubuwa 2 dake kashe yan Najeriya fiye da Boko Haram

Wani mashahurin Sarki a yankin Arewa ya gina rantsatstsen asibiti ga jama’ansa
Asibiti
Asali: UGC

Sai dai ba wannan bane karo na farko da Sarkin Gombe yake gudanar da irin aikace aikacen nan ba da yake zama gatan marayu da marasa karfi, inda ko a shekarar 2017 sai da ya sanya yara dubu uku (3,000) a makarantun firamari domin karfafa musu gwiwa su samu ilimi.

Baya ga sanya marayun makaranta, Sarkin ya rarraba musu kayayyakin karatu da suka hada da littafai da abin rubutu, inda yace ya yi musu wannan taimakko ne domin rage musu radadin talauci.

Haka zalika a shekarar 2017 ma sai da mai martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III ya samar ma matasa ashirin da takwas aiki a rundunar Sojan kasa da rundunar yansandan Najeriya.

Wani mashahurin Sarki a yankin Arewa ya gina rantsatstsen asibiti ga jama’ansa
Sarki
Asali: UGC

Sai dai wani abu dake daure ma jama’a kai shine har yanzu mai martaba Sarki ba shi da mata, kuma bai taba aure ba, duk kuwa da cewa shekarunsa 42 a rayuwa, da kuma mukaminsa na babban sarki a yankin Arewacin Najeriya.

Majiyoyi sahihai sun tabbatar da cewar a yayin da za’a nada shi sarautar Sarkin Gombe, an so a daura masa guda daga cikin yayan Sarkin Musulmi amma abin bai yiwu ba, haka zalika aurensa da diyar Sarkin Dukku, Gimbiya Aisha Musnan saura kiris, amma abin bai yiwu ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng