Wasu Musulman Turkiyya sun yi shekara da shekaru su na sallah ba tare da kallon Al-Qibla ba

Wasu Musulman Turkiyya sun yi shekara da shekaru su na sallah ba tare da kallon Al-Qibla ba

Mun samu wani labari mai ban mamaki cewa wasu Bayin Allah Masallata a can Kasar Turkiyya sun gano ashe tun da su ke sallah, ba gabas su ke kallo ba domin kuwa masallacin na su ya karkata daga Al-qibla.

Wasu Musulman Turkiyya sun yi shekara da shekaru su na sallah ba tare da kallon Al-Qibla ba
Musallata a Turkiyya sun shafe shekaru ba tare kallon Al-qibla ba
Asali: UGC

Masallaci Sugoren da ke kasar Turkiyya sun fahimci cewa sun yi shekaru fiye da 37 su na kallon wani bangaren da ya karkacewa Al-Qibla wajen sallah. An gina wannan masallaci ne a 1981 amma bai fuskanci ka’aba yadda ya kamata ba.

Wannan babban Masallaci da aka nada wani Matashi a matsayin sabon Limami kwanan nan ya gano cewa an dade ana salla a karkace. Wannan Limami mai suna Iman Kaya ya fara jin wannan magana ne kamar jita-jita a gari don haka ya bincika.

Ko da Ustaz Iman Kaya ya tambayi wani babban Malami a Garin Yalova, sai ya gano cewa ashe an dade a wannan Masallaci ba tare da ana kallon Gabas idan za ayi sallah ba. Jama’a dai sun fi shekara 37 su na sallah a jahilce a wannan Masallacin.

KU KARANTA: Ba za a taba raba Turai da addinin Musulunci ba Inji Kungiyar EU

Yanzu dai Limamin wannan Masallaci ya fadakar da kan Jama’a inda a maimakon a rusa Masallacin a sake gini, sai kurum aka yi ishara zuwa ga ainihin inda ya kamata Masallata su rika fuskanta ko yaushe idan su ka tashi za su yi Sallah a masallacin.

A addinin musulunci dai ana kallon Gabas ne inda Dakin Ka’aba yake idan za ayi kowace Sallah. A lokacin Manzon Allah Annabi Muhammad SAW ne aka canza wannan hukunci bayan an yi shekara da shekaru ana fuskantar Masallacin Garin Qudus.

Wani Bawan Allah ya bayyanawa ‘Yan Jarida cewa an taba rusa Masallacin a baya, a wancan lokaci ma dai an gano irin wannan kuskure ne na ganin cewa ana fuskantar wani barayin dabam ana sallah.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel