Hamshakin attajiri Dangote ya yi wani babban hubbasa wajen ciyar da ilimi gaba a Kano

Hamshakin attajiri Dangote ya yi wani babban hubbasa wajen ciyar da ilimi gaba a Kano

Shugaban jami’ar kimiyya ta jahar Kano dake garin Wudil, Alhaji Aiko Dangote, fitaccen attajiri dan asalin jahar Kano da yayi fice yayi zarra a nahiyar Afirka tare da suna a duk fadin Duniya, ya yi wani muhimmin aikin da zai kara cigaba ga harkar ilimi a jahar Kano.

Majiyar Legit.com ta ruwaito Aliko Dangote ya umarci hukumar jami’ar Wudil da ta dauki manyan malamai, gangaran ka fi gwani, wane gwani ciki fal shakku, watau Farfesoshi kenan guda goma sha biyar domin su koyar da dalibai tare da gogar da malaman jami’ar.

KU KARANTA: Karanta wasu muhimman bayanai 10 game da Hadiza sabuwar mataimakiyar Gwamna El-Rufai

Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Shehu Alhaji ne ya sanar da haka a ranar Juma’a, 2 ga watan Nuwamba, a yayin da yake ganawa da manema labaru, inda yake bayyana wasu muhimmancin cigaban da jami’ar ta samu a yan shekarunnan.

Farfesa Alhaji ya bayyana cewa tsarin da Dangote ya bullo da shi shine, zai biya Malaman albashin har na tsawon shekary hudu, yayin da suke koyarwa a jami’ar, bugu da kari akwai yiwuwar zai sabunta yarjejeniyar zuwa shekaru takwas.

Bugu da kari mashahurin attajirin ya dauki alkawarin kula da walwalar Malaman su goma sha biyar, inda ya baiwa hukumar jami’ar tabbacin zai gina ma Malaman gidajen zamansu a cikin jami’ar, tare da sanyan musu duk abubuwan jin dadi a gidajen.

A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Kano a karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganude ta dauki sabbin malamai guda dari shida da zasu dinga koyar da daliban jami’ar, kamar yadda Farfesa Alhaji ya bayyana.

Farfesa Alhaji yace gwamnatin jahar Kano ta dauki malaman ne da nufin zaburar da jami’ar domin tayi ma sa’o’inta zarra a dukkanin fanonin karatun kimiyya da binciken ilimi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel