Ku bar garinku tun kafin mu dirar ma ku - 'Yan bindiga sun bawa jama'a a Katsina wa'adin
- Fiye da mutane 1,000, maza da mata, ne su ka tashi daga kauyen Damburawa tare da komawa fadar hakimin Batsari a jihar Katsina
- Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya bayyana cewar 'yan bindigar sun kai hari kauyen amma sai jama'ar garin su ka dakile harin tare da kama biyu daga cikin maharan
- Alhaji Mansur Muaza, shugaban rikon kwarya na karamar Batsari, ne ya shaidawa manema labarai hakan a yau, Alhamis
Fiye da mutane 1,000, maza da mata, ne su ka tashi daga kauyen Damburawa tare da komawa fadar hakimin Batsari a jihar Katsina bayan samun barazana daga 'yan bindiga.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya bayyana cewar 'yan bindigar sun kai hari kauyen amma sai jama'ar garin su ka dakile harin tare da kama biyu daga cikin maharan.
Alhaji Mansur Muaza, shugaban rikon kwarya na karamar Batsari, ya shaidawa manema labarai a yau, Alhamis, cewar 'yan bindigar sun aiko da takardar barazanar cewar za su dawo daukan fansa.
Muaza ya bayyana cewar karamar hukumar ce ke ciyar da mutanen tun bayan yin hijirar su daga kauyen ranar Laraba.
"Mun ankarar da jami'an tsaro abinda ke faruwa kuma tuni sun tura dakarunsu da ke sintiri a yankin da kewaye domin tabbatar da ba a samu wata matsala ba.
DUBA WANNAN: Sojoji sun gano wani haramtaccen sansanin bayar da horo a arewa
."Kazalika mun samar da wasu jami'an tsaro da ke gadin jama'ar kauyen da yanzu haka ke zaman gudun hijira a fadar hakimi," in ji Muaza.
Shugaban karamar hukumar ya bukaci 'yan gudun hijirar su kwantar da hankalinsu tare da tabbatar ma su da cewar gwamnatin jihar Katsina za ta tabbatar da tsaron lafiyar su da dukiyoyin su.
NAN ta rawaito cewar 'yan bindiga na cigaba da addabar jama'ar kananan hukumomin Safana, Batsari, da Danmusa da satar mutane domin neman kudin fansa a kullum.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng