Bulalar Sharo ta salwantar da rayuwar wani Bafulatani a jihar Jigawa
Da sanadin shafin jaridar Premium Times mun samu rahoton cewa, bulalar sharo ta salwantar da rayuwar wani Matashi yayin gudanar da bikin al'adar Fulani na shekara a kauyen Kontoga dake karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa.
Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Audu Jinjiri, shine ya bayar da shaidar hakan yayin ganawarsa da manema labarai a ranar Larabar ta gabata.
Rahotanni sun bayyana cewa, wani Matashi Abdullahi Ibrahim daga karamar hukumar Takai ta jihar Kano ya jagoranci tawagar Matasa domin halartar wannan bikin al'adar Fulani na Sharo inda rai ya yi halinsa ga daya daga cikin su.
Matasan daga jihar Kano da suka halarci wannan bikin al'ada da aka saba gudanarwa a kowace sun hadar da Ruwaji Maikudi, Ibrahim Lawal da kuma Hussaini Adamu wanda dukkanin su ba su haura shekaru 23 da haihuwa ba.

Asali: Facebook
Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, Matasan daga jihar Kano sun fafata da abokanan wannan gasa ta Sharo, inda bayan Ruwaji ya sha shimfidar bulalai a hannun wani Matashi Ibrahim Auwal daga jihar Bauchi ya fadi kansa wanwar da sai gadon asibiti ya tsinci kansa.
KARANTA KUMA: Har yanzu ba mu da wani zabi tsakanin Buhari ko Atiku - Matasan Arewa
Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, rai ya yiwa Ruwaji halinsa bayan garzayawa da shi zuwa asibiti na kurkusa da wannan lamari ya sanya Ibrahim ya ce kafa mai na ci ban baki ba.
Wannan bikin al'ada da ya saba gudana a kowace shekara na daukar hankalin dumbin al'umma daga jihohin Bauchi, Kano da kuma Jigawa inda Fulani ke baja kolin bajinta da kuma jarumtar su.
Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng