Mutane 360 sun bakunci lahira a cikin wata guda a wasu Jihohin kasar nan
Mun ji cewa Rahotannin da wata Kungiya ta kasar waje ta fitar kwanan nan ya nuna cewa ‘Yan ta’adda sun kashe fiye da mutane sama da 300 a cikin wata daya rak a wasu manyan Jihohi na Arewacin Najeriya.
Wata kungiya mai suna “International Society for Civil Liberties and Rule of Law” tace ‘Yan ta’adda da masu tada rikicin Kabilanci sun kashe Bayin Allah akalla 300 a cikin watan jiya a Yankin Adamawa, Kaduna, Benuwai da Filato.
Shugaban wannan Kungiya da tayi wannan bincike, Emeka Umeagbalasi ya bayyana cewa daga cikin wadanda aka kashe akwai Kiristoci kusan 260 da kuma Musulmai fiye 100. Daga cikin har da hare-haren Boko Haram a Jihar Borno.
An dai fi yin barnar ne a irin su Jihar Kaduna, inda aka kashe mutane akalla 135 daga tsakiyar Watan na Oktoba zuwa karshen Watan da ya shude jiya. Hakan ya sa Gwamnan Jihar ya tashi tsayin-daka wajen ganin an samu zaman lafiya.
KU KARANTA: Adadin matsiyata yana karuwa a Najeriya a mulkin Buhari
A rahoton da aka saki jiya, mun ji cewa an kuma kashe Bayin Allah sama da 50 a Garin Jos sannan kuma an kona dakunan addini da dama a cikin Jihar na Filato. Haka-zalika kuma an kashe mutane fiye da 10 a wasu Garuruwa a Jihar Benuwai.
A baya dai hasashe sun nuna cewa akalla ana kashe mutane 10 a kowane wata a irin su Jihar Folato, Nasarawa, Benuwai da kuma Kaduna da ke cikin Arewacin kasar. Gwamnatin Buhari dai tayi alkawarin gyara sha’anin tsaro a fadin Najeriya.
A Jihar Borno kuma inda ‘Yan ta’addan Boko Haram su ka dade su na ta’asa musamman kafin zuwan wannnan Gwamnati, an aika mutane kusan 40 a lahira a wani Yanki na Karamar Hukumar Jere.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng