Hotunan makaman da aka kama 'yan Shi'a da su a Abuja

Hotunan makaman da aka kama 'yan Shi'a da su a Abuja

- A jiya, Talata, ne aka yi wani kazamin artabu tsakanin jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya da mabiya Shi'a a Abuja

- Hukumar ta 'yan sanda ta yi bajakolin mabiya Shi'ar da ta kama tare da makaman da ta samu a tare da su

- 'Yan Shi'ar sun kona daya daga cikin motocin jami'an 'yan sanda yayin rikicin na jiya

A jiya, Talata, ne aka yi wani kazamin artabu tsakanin jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya da mabiya Shi'a a Abuja.

A yayin gwabzawar, jami'an 'yan sanda sun yi nasarar cafke mabiya Shi'a kimanin 400 tare da tsare su a ofishinsu.

Hukumar ta 'yan sanda ta yi bajakolin mabiya Shi'ar da ta kama tare da makaman da ta samu a tare da su.

Daga cikin irin wadannan makamai da aka samu a wurin mabiya Shi'ar akwai bam din kalanzir na kwalba da miyagun kwayoyi da ke birkice tunani.

Hotunan makaman da aka kama 'yan Shi'a da su a Abuja
Hotunan makaman da aka kama 'yan Shi'a da su a Abuja
Asali: Facebook

Hotunan makaman da aka kama 'yan Shi'a da su a Abuja
Hotunan makaman da aka kama 'yan Shi'a da su a Abuja
Asali: Facebook

Hotunan makaman da aka kama 'yan Shi'a da su a Abuja
Motar 'yan sanda da 'yan Shi'a da su ka kone a Abuja
Asali: Twitter

'Yan Shi'ar sun kona daya daga cikin motocin jami'an 'yan sanda yayin rikicin.

Ko a ranar Litinin sai da dakarun sojin Najeriya su ka budewa wasu 'yan Shi'a wuta bayan sun tare hanyar da motar sojoji dauke da malamai za ta wuce a kan titin Nyanya.

DUBA WANNAN: Alkawarin da Buhari ya yiwa 'yan takarar APC da su ka fadi a zaben cikin gida

Haka a ranar Juma'a ta makon jiya aka kara samun kwatankwacin irin wannan rikicin tsakanin dakarun soji da mabiya Shi'ar a daidai Zuba, kan hanyar shiga Abuja.

Duk da wannan gwabzawa, mabiya Shi'ar sun ce ba zasu daina zanga-zanga ba har sai an sako jagoransu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, da gwamnati ke tsare da shi tun shekarar 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel