Yadda binciken Sojoji ya kaisu ga bankado inda aka boye gawar janar Alkali

Yadda binciken Sojoji ya kaisu ga bankado inda aka boye gawar janar Alkali

Rundunar Sojan kasa ta sanar da gano gawar wani babban hafsan Soja, kuma shugaban mulki da kudi a shelkwatar rundunar, Manjo Janar Idris Alkali, a cikin wata tsohuwar rijiya a kauyen Dura Du dake cikin karamar hukumar Jos ta kudu.

Kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito a ranar 3 ga watan Satumba ne aka nemi Alkali aka rasa, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa jahar Bauchi, tun daga rannan ne fa Sojoji da sauran jami’an tsaro suka shiga nemansa.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Gwamnatin tarayya ta yi watsi da bukatar gwamnoni akan karancin albashi

Yadda binciken Sojoji ya kaisu ga bankado inda aka boye gawar janar Alkali
Gawar janar Alkali
Asali: Facebook

Majiyar Legit.com ta ruwaito babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bada umarnin a yi ta bincike har sai an gano janar Alkali ko gawarsa a duk inda yake, inda Sojojin suka karkatar da binciken nasu ga garin Dura-Du.

Bayan makonni biyu ana gudanar da binciken sai Sojoji suka yashe wani rafi dake tsakiyar garin, bayan wasu gungun mata sun gudanar da zanga zanga cewa rafin bauta ne don haka kada wanda ya taba shi, amma Sojoji suka yi gaban kansu, a ciki suka gano motar mamacin da wasu motoci biyu.

Yadda binciken Sojoji ya kaisu ga bankado inda aka boye gawar janar Alkali
Rijiyar
Asali: UGC

Kwamandan Sojoji na rukuni na 3 dake garin Jos, Birgediya Janar Umar Muhammed ya bayyana cewa wani daga cikin wadanda suka kama ne ya kaisu ga rijiyar da suka ga wani kabari da aka binne Alkali, amma daga bisani suka jefa shi cikin rijiya.

Muhammed ya gode ma rundunar Yansandan Najeriya da hukumar kwana kwana bisa gudunmuwar da suka basu tun daga farkon fara wannan bincike har zuwa lokacin da aka gano gawar mamacin. Ya kaar da cewa tsuguni bata kare ba.

“Babban hafsan Sojan kasa ya bamu umarni guda uku, mu gano Alkali ko da rai ko ba rai, mu gano motarsa, sa’annan mu kama tare da tabbatar da an hukunta duk wanda keda hannu a cikin lamarin. A yanzu mun cika umarni biyu, saura na ukun.

“Ba zamu huta ba har sai mun cika umarnin nan uku gaba daya, muna tabbatar ma duk wadanda suka tsere cewa zamu cimmasu a duk inda suke shiga.” Inji shi. Daga karshe manyan Sojoji sun yi ma gawar Alkali fareti, sa’annan aka tafi da ita.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel