Kar ku zabi Atiku a 2019 - Dan Lamidon Adamawa

Kar ku zabi Atiku a 2019 - Dan Lamidon Adamawa

Wata kungiyar siyasa, "Operation Deliver Your Unit (ODYU), karkashin jagorancin yariman fadar Lamidon Adamawa, ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kayar da wazirin Adamawa, kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a jihar sa ta haihuwa.

Kungiyar ta yi ikirarin yin aiki domin tabbatar da nasarar Buhari a karkashin jam'iyyar APC a zaben shekarar 2019 tare da yin kira ga jama'a da kar su zabi Atiku.

ODYU, kungiyar da dan sarkin Yola (Lamidon Adamawa) kuma kwamishinan harkokin kananan hukumomin jihar Adamawa, Mohammed Barkindo, na da magoya baya kimanin 2,609 da su ka fito daga mazabun da ke fadin jihar Adamawa.

Jama'a na mamakin yadda Barkindo ke adawa da Atiku, kasancewar sa dan asalin jihar Adamawa kuma waziri ga mahaifinsa, sarkin Yola.

Kar ku zabi Atiku a 2019 - Dan Lamidon Adamawa
Lamidon Adamawa
Asali: Facebook

"Babu kokwanto a kan nasarar Buhari a zaben shekarar 2019. Muna jiran rantsuwa ne da rabon mukamai," kamar yadda Barkindo ya fada a bainar jama'a yayin wani taro.

A nasa bangaren, sakataren kungiyar, Ahmed Lawan, ya bukaci jama'ar Adamawa su dauki Buhari tamkar dan asalin jihar.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi muhimmiyar ganawa da 'yan takarar APC

"Na ji wasu na maganar cewa dan takarar PDP dan jihar Adamawa ne, amma ina son sanar da ku cewar Buhari ma dan jihar Adamawa ne saboda matar sa.

"Bayan hakan shugaba Buhari ya yiwa jihar Adamawa aiyukan da 'yan jihar da su ka samu dama su ka gaza yi ma mata," a cewar Lawan.

Kungiyoyin da ke goyon bayan 'yan takarar biyu; Atiku da Buhari, na cigaba da fitowa domin tallata dan takarar su

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng