Babbar magana: INEC ta gargadi Amurka, Ingila da Rasha a kan zaben 2019
- Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ta bayyana fargabar yin kutse a cikin sakamakon zaben ta yanar gizo
- Farfesa Yakubu ya yi wannan kalamai ne ta bakin wakilinsa yayin wani taro a kan yada labarai da aka yi a ofishin kungiyar kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) da ke Abuja
- Ko a yanzu haka kasar Amurka na binciken yadda kasar Rasha ta yi ma ta cikin sakamakon zaben shugaban kasa
A yayin da kullum zaben shekarar 2019 ke kara matsowa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana fargabar a kan yiwuwar yin kutse a cikin sakamakon zaben shugaban kasa ta yanar gizo.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ne ya bayyana hakan ranar Litinin a Abuja.
Ya gargadi manyan kasashen, gabashin Amurka, da Rasha a kan su kwana cikin shirin cewar Najeriya ba zata yarda da katsalandan a sakamakon zaben 2019 ba.
Farfesa Yakubu ya yi wannan kalamai ne ta bakin wakilinsa yayin wani taro a kan yada labarai da aka yi a ofishin kungiyar kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) da ke Abuja.
Ya kara da batun yin kutse a sakamakon zabe ta hanyar yana gizo wani abu ne da tilas a yi kokarin dakile shi.
Ko a yanzu haka kasar Amurka na binciken yadda kasar Rasha ta yi ma ta cikin sakamakon zaben shugaban kasa.
Dakta Lecky Mustapha, wakilin Farfesa Yakubu, ya lissafa ragowar kalubale da zabe ke fuskanta da su ka hada da yada labaran karya, musamman a sabbin kafafen yada labarai.
DUBA WANNAN: Kare jini biri jini: Mabiya Shi'a sun cinnawa motar 'yan sanda wuta a Abuja a sabuwar zanga-zanga, hotuna
Kazalika ya bukaci 'yan jarida da su nuna kwarewa da yin aiki da dokokin aikin jarida a lokacin zabe.
Taron da kasar kasar Jamus ta bayar da gudunmawa wajen shiryawa, ya samu halartar wakilai daga kasashen Afrika ta yamma.
A wani labarin mai nasaba da wannan, shugaba Buhari ya lashi takobin gudanar da zabe na gaskiya da adalci a shekarar 2019.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng