Real Madrid ta sanar da sabon mai horas da yan wasa, karanta abubuwa 10 game da shi

Real Madrid ta sanar da sabon mai horas da yan wasa, karanta abubuwa 10 game da shi

Hukumar kungiyar kwallon kafa ta Real Marid ta sanar da sunan Santiago Solari a matsayin sabon mai horas da yan wasanta bayan sallamar Julen Lopetegui da ta yi daga mukamin, sakamakon ya gaza tabuka wani abin kirki bayan watanni 5 da nada shi.

Sallamar Julen ya tabbata ne bayan Real ta sha kashi a hannun abokiyar adawarta, Barcelona a wasan da suka buga a ranar Lahadin data gabata, inda Barcelona ya lallasa Real da ci 5-1, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi garkuwa da wani malamin jami’ar jahar Adamawa, Farfesa Allan

Da wannan ne majiyar Legit.com ta kawo muku wasu alkalumma guda goma dangane da sabon kociyan, Santiago Solari:

Real Madrid ta sanar da sabon mai horas da yan wasa, karanta abubuwa 10 game da shi
Solari
Asali: Twitter

- A shekarar 1976, 7 ga watan Oktoba aka haife shi

- Ya buga ma kasar Ajantina kwallo

- Ya yi karatu a kwalejin Richard Stockon dake New Jersey

- Ya fara kwallo a sifen a shekarar 1999 a kungiyar Atletico Madrid

- Ya koma kungiyar Real Madri a shekarar 1999

-Ya koma kungiyar Inter Milan a shekarar 2005

- Wasanni 11 kacal ya buga ma Ajantina

- Kwararren dan kwallo ne da ya shahara wajen yanka yan wasa

- Ya shiga harkar horas da yan wasa a shekarar 2013 da matasan yan kwallon Real Madrid

- A ranar 29 ga watan Oktoba aka nada shi mukamin riko na mai horas da Real Madrid

A yanzu dai, daga magoya har shuwagabannin kungiyar Real Madrid na fatan ganin Solari ya ceto kungiyar daga mawuyacin halin da ta shiga, inda a ta samu maki goma sha hudu a wasanni goma sha hudu da ta buga a karkashin Julen.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel