Kungiyar Real Madrid ta kiro kocinta, ta nada tsohon dan wasanta

Kungiyar Real Madrid ta kiro kocinta, ta nada tsohon dan wasanta

- Kungiyar ta Madrid ta yanke shawarar korar Lopetegui ne bayan ya yi rashin nasara a wasanni 5 a cikin 7 da ya jagoranci kulob din

- Kungiyar ta amince da damka kungiyar, na wucin gadi, a hannun tsohon dan wasan ta, Santiago Solari

- A jiya ne kungiyar Madrid ta debi kashinta a hannun abokiyar hamayyar ta, kungiyar Barcelona, da ci 5 da 1

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da ke kasar Spain ta kori kocinta, Julen Lopetegui, bayan shafe kwanaki 139 kacal da fara aiki tare da kungiyar.

Kungiyar ta Madrid ta yanke shawarar korar Lopetegui ne bayan ya yi rashin nasara a wasanni 5 a cikin 7 da ya jagoranci kulob din.

Kungiyar ta amince da damka kungiyar, na wucin gadi, a hannun tsohon dan wasan ta, Santiago Solari.

Kungiyar Real Madrid ta kiro kocinta, ta nada tsohon dan wasanta
'Yan wasan Kungiyar Real Madrid
Asali: Getty Images

A jiya ne kungiyar Madrid ta debi kashinta a hannun abokiyar hamayyar ta, kungiyar Barcelona, da ci 5 da 1.

DUBA WANNAN: Kisan dan sanda: Tsohon shgaban majalisa da ragowar wasu mutane sun shiga hannu

Kungiyar ta yanke shawarar sallamar Lopetegui da nada Solari ne bayan ganawar da masu Kulob din su ka yi a daren yau, Litinin.

Solari zai fara jagorantar kungiyar Madrid a wasan da zata buga a gasar cin kofin Copa del Rey da za ta buga da kungiyar Melilla ranar Talata. Ana saka ran shine zai jagoranci kungiyar a wasanta na gasar Laliga da kungiyar Valladolid, ranar Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng