Rai bakon duniya: Yadda tsawa mai karfi ya halaka wani Uba da dansa

Rai bakon duniya: Yadda tsawa mai karfi ya halaka wani Uba da dansa

Wani abin tausayi da ban al’ajabi ya faru a kasar Uganda a karshen makon data gabata, ranar Lahadi 28 ga watan Okotoba, inda wan wani mutumi da Dansa suka yi mutuwar ba zata a daidai lokacin da tsawa ya fada musu, inji rahoton Punch.

Majiyar Legit.com ta ruwaito wannan lamari mai muni ya faru ne a kauyen Lumodo dale yankin Lamwo na kasar Uganda, inda mamatan suke zama a gidansu, sai tsawar ta fada musu da misalin karfe 4:30 na rana yayin da ake kwarara ruwan sama kamar da bakin kwarya.

KU KARANTA: Babban jirgin sama makare da fasinjoji ya fada cikin ruwa, kowa da kowa ya mutu

Wannan lamari ne ya sabbaba mutuwar Uban mai suna David Obwor da dansa George Obalim mai shekau goma, sa’annan tsawar ya jikkata wasu mutane uku daban, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Rahoton da majiyarmu ta dauko ya bayyana sunayen sauran mutane ukun da suka jikkata sun hada da Bosco Olol, mai shekaru 40, Jennifer Abwor da karamin yaro mai shekaru biyar, Jalo.

Shugaban karamar hukumar Lamwo, George Nyeko ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Lukung, kuma suna samun sauki.

Shugaban yayi Karin haske game da yadda lamarin ya auku, inda yace mutanen suna zaune ne a karkashin wata bishiya a yayin da ake ruwan sama ne lokacin da aka yi tsawar, nan take tsawar ta fada musu.

Sanannen abu ne a kasar Hausa cewa tsawa ko aradu na faduwa ne a kan bishiya, musamman ma bishiyoyin dake cikin kungurmin daji, don haka ne iyaye da magabata ke gargadin yara akan zama a kasan bishiya ko kusantar bishiya a lokacin da ake ruwan sama.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng