Shugaban kasa zai zauna da manyan APC saboda gudun sauyin-sheka kafin 2019

Shugaban kasa zai zauna da manyan APC saboda gudun sauyin-sheka kafin 2019

- Buhari zai gana da Shugaban APC na kasa Oshiomhole saboda rikicin Jam’iyya

- Tuni an sa a duba rigimar da ta barko cikin APC bayan zabukan fitar da gwani

Shugaban kasa zai zauna da manyan APC saboda gudun sauyin-sheka kafin 2019
Buhari zai gana da Shugaban APC domin hana manyan Jam’iyya barin APC
Asali: Depositphotos

A cikin makon nan ne kowace Jam’iyya za ta mikawa Hukumar zabe na kasa INEC cikakken sunayen ‘Yan takaran ta. Hakan ta sa Buhari ya shirya zama da manyan Jam'iyyar APC domin dinke duk wata baraka da za ta tashi.

Nan ba da jimawa ba Shugaba Buhari zai gana da Adams Oshiomhole wanda shi ne Shugaban APC na kasa baki daya domin ganin babu wadanda su ka sauya-sheka daga Jam’iyyar APC yayin da ake shiryawa zaben 2019.

KU KARANTA: Buhari ya bukaci yan Nigeria su zabi APC don gujewa kuskuren 1999 da aka yi a baya

Rikici dai ya barke a APC a Jihohi irin su Ogun, Adamawa, Bauchi, Jigawa, Imo, Ondo, Kebbi da kuma Kano saboda zabukan tsaida ‘Yan takara. Yanzu haka dai idan aka yi sake wasu manyan ‘Yan APC na iya sauya-sheka.

Tuni dai Shugaban kasa Buhari ya sa wasu mutane 5 su sasanta kan ‘Yan APC. Daga cikin wadanda su ke cikin kwamitin akwai Adamu Adamu, da Abubakar Malami da kuma Abba Kyari kamar yadda mu ka samu labari.

Akwai Gwamnonin APC irin su Rochas Okorocha, Abdulaziz Yari, Rotimi Akeredolu da kuma Ibikunle Amosun wadanda ba su ji dadin sakamakon zabukan da aka gudanar ba. APC dai za tayi kokarin shawo kan Gwamnonin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng