Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da goyon bayan masu sana'ar nishadantarwa a Najeriya - Osinbajo

Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da goyon bayan masu sana'ar nishadantarwa a Najeriya - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayar da tabbacin jajircewa da goyon bayan gwamnatin tarayya ga dukkanin masu ruwa da tsaki a harkokin sana'ar nishadantarwa domin kawo inganta kawo ci gaban kasa.

A ranar Juma'ar da ta gabata Osinbajo ya bayar da wannan tabbaci yayin wani taro da kungiyar masu sana'ar nishadantarwa ta dauki nauyin gudanar a jihar Legas.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, daruruwan masu sana'ar nishadida suka hadar da jaruman fina-finai, masu barkwanci, mawaka da makamantansu sun halarci wannan babban taro.

Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da goyon bayan masu sana'ar nishadantarwa a Najeriya - Osinbajo
Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da goyon bayan masu sana'ar nishadantarwa a Najeriya - Osinbajo
Asali: Depositphotos

Mataimakin shugaban kasar yake cewa ba bu wani fitaccen dan siyasa mai hankali da zai yanke alakarsa da masu sana'ar nishadantarwa hakazalika ba za su watsar da 'yan siyasa ba sakamakon dangartaka ta cude ni in cude ka dake tsakanin su.

KARANTA KUMA: Hukumar Sojin Kasa za ta fara kera Motocin Yaki a 2025 - Buratai

A yayin da Farfesa Osinbajo ya lura da yadda wasu masu sana'ar nishadi tuni suka damalmala a cikin harkokin siyasa, ya nemi sauran da su yi koyi da abokanan sana'arsu domin kawo sauyi mai tasirin gaske a kasar nan.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Sarkin Kano Muhammadu Sanusu II, ya shawarci al'ummar kasar akan kauracewa zaben shuwagabanni da suka gaza gabatar da takardun shaidar karatu da ma su takardun bogi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel