A karshe: Ciyamomin APC sun bayyana manufar ma su son a tsige Oshiomhole

A karshe: Ciyamomin APC sun bayyana manufar ma su son a tsige Oshiomhole

- Rikicin APC tsakanin wasu daga cikin gwamnonin jam'iyyar na cigaba da kara zafi

- Wasu mambobin jam'iyyar APC da ke goyon bayan Oshiomhole na cigaba da yin fassara a kan yunkurin tsige shi

- Ko a ranar Alhamis sai da Sanata Marafa ya zargi gwamna Yari na Zamfara da zama a sahun gaba wajen kulle-kullen kawar da Oshiomhole

Shugabannin jam'iyyar APC 5 daga jihohin yankin kudu maso kudu sun bayyana ma su kira da yunkurin son a tsige Oshiomhole da cewar makiya shugaba Buhari ne.

Ciyamomin sun bayyana matsayar su ne a cikin wani sako da su ka fitar bayan kammala wani taron shugabannin jam'iyyar APC na jihohin Neja-Delta a Abuja.

Takardar sanarwar na dauke da sa hannun Jones Ode Erue, shugaban jam'iyyar APC a jihar Delta; Honarabul Ini Okopido, shugaban jam'iyyar APC a jihar Akwa Ibom; Honarabul Amos Jothan, shugaban jam'iyyar APC a jihar Bayelsa da Dakta Matthew Achigbe, shugaban jam'iyyar APC a jihar Kuros Riba.

A karshe: Ciyamomin APC sun bayyana manufar ma su son a tsige Oshiomhole
Oshiomhole
Asali: Depositphotos

"Mu na tare da shugabancin jam'iyyar APC karkashin Kwamred Adams Oshiomhole kuma za mu tirjewa duk wani yunkuri na raba kan jam'iyyar APC. Duk ma su yunkurin tsige Oshiomhole na yi ne saboda son rai da kokarin kawowa APC cikas a zaben shekarar 2019, amma ba zamau bari su yi nasarar hakan ba.

DUBA WANNAN: Yunkurin tsige Oshiomhole: Sanatan Zamfara ya tona asirin gwamna Yari

"Muna sane da shirin su na son kawowa takarar shugaba Buhari nakasu.

"Muna kira ga gwamnonin, shugabanni da masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC da mu hada kanmu tare da goyawa Oshiomhole baya," kamar yadda ya ke a cikin sanarwar.

Kazalika ciyamomin sun jaddada goyon bayansu ga Oshiomhole da kuma takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng