Na saba lalata da matan aure amma ina son dainawa - matashi dan Najeriya

Na saba lalata da matan aure amma ina son dainawa - matashi dan Najeriya

Batun cin amanar aure dai wani laifi ne da yawanci aka fi samun maza da aikata shi. Sai dai Bahaushe na cewa sai bango ya tsage kadangare ke samun wurin shiga domin matan ne ke bawa maza kafar da zasu samu damar yin lalata da su.

Irin lamari ne ta kai ga wani kyakykyawan matashi a Najeriya, Kolade Babajide, ya fito fili ya shaidawa duniya cewar yana kwanciya da matan aure tare da bukatar neman taimako domin ya daina wannan hali.

Na saba lalata da matan aure amma ina son dainawa - matashi dan Najeriya
Matashi dan Najeriya, Kola Babajide
Asali: Facebook

Na saba lalata da matan aure amma ina son dainawa - matashi dan Najeriya
Rubutun Kola Babajide a shafinsa na Facebook
Asali: Facebook

Matashin, da yanzu haka ke zaune a Ingila, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook tare da sanar da cewar yanzu haka yana neman taimako domin ya daina wannan hali duk yana jin dadin abin da yake aikatawa.

DUBA WANNAN: Babban abin da ya girgiza ni a matsayina na mataimakin shugaban kasa - Osinbajo

A cewar Babajide, "na saba yin lalata da matan aure. Su kan neme ni kamar yadda nima nake nemasu. Ina son na daina wannan hali. Ba zan yi karya ba, ina jin dadin harka da matan auren amma duk da haka ina son dainawa.

Na saba lalata da matan aure amma ina son dainawa - matashi dan Najeriya
Kolade Babajide
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng