Magudin zabe: Masu zanga zanga sun yi ma fadar gwamnatin jahar Nejah tsinke

Magudin zabe: Masu zanga zanga sun yi ma fadar gwamnatin jahar Nejah tsinke

A yanzu dai a iya cewa ta tabbata zaben fidda gwani na jam’iyyar APC ta wuce amma fa ta bar baya da kura, musamman yadda kusan dukkanin jihohin da APC take mulki babu inda ba’a samu zargin ka ci, baka ci ba, baja ci ba, ka ci.

Jihohin da matsalolin nan suka fi kamari basu wuce jihohin Zamfara da Imo ba, inda a yanzu haka hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana cewa ba za taba yarda jam’iyyar APC ta tsayar da yan takarkaru na kowani mukami ba.

KU KARANTA: Kallabi tsakanin rawwuna: Mace ta zama shugabar wata kasar Afirka a wani yanayi na rabo

Sai dai yayin da aka samu sulhu da kwanciyar hankali a tsakar gidar jam’iyyar APC ta jahar Imo, lamarin ba haka yake ba a jahar Neja dake yankin Arewa ta tsakiya, inda wasu yayan jam’iyyar suka zargi gwamna jahar da kwace musu abinda suka zaba.

Magudin zabe: Masu zanga zanga sun yi ma fadar gwamnatin jahar Nejah tsinke
Yayan APC
Asali: Twitter

Ireiren yayan jam’iyyar ne a yau Alhamis 25 ga watan Oktoba suka fita zanga zangar nuna rashin jin dadinsu da bisa zargin da suke ma gwamnan jahar, Sani Bello na cewa ya canza musu dan takarar da suka zaba a zaben kato bayan kato da suka yi.

Guda daga cikinsu ya bayyana ma majiyar LEGIT.com cewa dan takararsu Jaafaru Iliyasu Auna ne ya lashe zaben fidda gwanin dan takarar kujerar dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Magama/Mariga/Rijau, amma sai aka canza shi da Shehu Saleh shalelen gwamnan.

Daga karshe har ta kai ga masu zanga zanga suna zargin cewa hukumar zabe ta amshi takardar tabbatar da takara wanda ta baiwa Jaafaru Iliyasu Auna tun a farko sakamakon murdiyar da suka ce Gwamna Sani ne da kansa ya jagoranci tafkawa.

Daga jihohin da rikicin zaben fidda gwani na APC yayi karfi akwai jahar Kaduna, jahar da aka ja daga tsakanin gwamnan jahar, Malam Nasir Ahmad El-Rufai da Sanatan jam’iyyar, Shehu Sani wanda a yanzu haka ya fice daga APC saboda ya lura bata bashi takarar Sanata ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng