Tashin hankali: 'Yan fashi sun sace bindigu masu yawa daga ma'ajiyar makaman 'yan sanda
- 'Yan fashi sun wawashe bindigogi daga ma'ajiyar makaman 'yan sanda da ke garin Gonja a Ghana
- Kakakin hukumar 'yan sandan yankin DSP Mohammed Tanko ya tabbatar da afkuwar lamarin
- DSP Mohammed Tanko ya ce hukumar ta fara bincike domin gano yadda 'yan fashin suka samu damar aikata satar
Wasu da ake kyautata zaton 'yan fashi da makami ne suka kai farmaki ma'ajiyar makamai na 'yan sanda da ke Daboya a Arewacin Yankin Gonja da ke Ghana inda suka sace Ak 47 guda biyu da kuma 'shotgun' guda daya.

Asali: Twitter
Jami'an 'yan sanda na yankin tuni sun fara bincike domin gano yadda 'yan fashin suka samu damar aikata wannan fashin kamar yadda Punch ta ruwaito.
DUBA WANNAN: EFCC ta kama dan takarar gwamna a Kano bisa laifin damfarar N100m
Kakakin 'yan sanda na yankin Arewacin kasar, DSP Mohammed Tanko ya tabbatar da afkuwar lamarin da ya ke zantawa da Citi News, ya kuma ce dukkan yan sandan da ke yankin suna cikin shiri domin binciko wanda suka aikata laifin.
"Muna gudanar da bincike domin gano yadda 'yan fashin suka shiga ma'ajiyar. Muna bincike domin gano ko dan sandan da ke gadin wurin yana barci ne ko kuma bai zo aiki ba ko kuma ya yi tafiyarsa yawo ne domin 'yan fashin su samu damar aikata satar," Inji Mohammed
Kwamandan yankin ya bayar da umurnin ga dukkan 'yan sandan da ke Damango da Daboya su tsaurara sinitiri a yankin musamman kan manyan tituna domin su kama 'yan fashi idan sunyi yunkurin amfani da bindigogin domin yiwa matifya fashi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng