Kallabi tsakanin rawwuna: Mace ta zama shugabar wata kasar Afirka a wani yanayi na rabo

Kallabi tsakanin rawwuna: Mace ta zama shugabar wata kasar Afirka a wani yanayi na rabo

Da safiyar yau ne aka rantsar da uwargida Sahle-Work Zewde a matsayin shugabar kasar Habasha watau Ethopia, biyo bayan murabus da Mulatu Teshome yayi a matsayin shugaban kasar a ranar Laraba, kamar yadda gidan Talabijin na Channels ta ruwaito.

Majiyar LEGIT.com ta ruwaito Uwargidar Sahle kwararriyar ma’aikaciyar diflomasiyya ce, inda ta zama jakadiyar kasar Habasha ga kasashe da dama da suka hada da Djibouti, Faransa, Sanigal da wata kungiyar kasashen gabashin Afirka a lokuta daban daban.

KU KARANTA: Allah ya kiyaye gaba: Anyi mummunar hatsari shanu a jahar Legas (Hotuna)

Jim kadan da samun wannan cigaba, Uwargida Sahle ce wakiliyar majalisar dinkin duniya a kungiyar kasashen Afirka, AU, sa’annan rahotanni sun bayyana cewa baya ga sanin aiki, Mulatu ta kware a harsunan Turanci, Faransa da Amharic.

Kallabi tsakanin rawwuna: Mace ta zama shugabar wata kasar Afirka a wani yanayi na rabo
Uwargida Sahle
Asali: Facebook

Wannan mukami da Sahle ta yi dare dare akai zai bata damar shafe tsawon shekaru goma sha biyu akan karagar mulki idan har tafiya tayi dadi, saboda ba ita bace babbar shugabar kasar, akwai mukamin Firai minista, wanda Abiy Ahmed ke rike da shi.

A irin wannan tsarin mulkin, Firai minista ne shugaba mai cikakken iko, shi kuwa shugaban kasa watau President ayyukansa basu wuce wakiltar shugaba mai cikakken iko ba a wuraren taruka daban daban.

A satin daya gabata ne shugaba Abiy Ahmed ya nada sabbin Ministoci guda ashirin, inda mata suka kwashe rabin mukaman, daga ciki har ma’aikatar tsaro inda Aisha Muhammed ta zama sabuwar minista, da ma’aikatar zaman lafiya wanda take kula da Yansanda da hukumar leken asiri a karkashin ikon Muferiat Kamil.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng