Allah ya kiyaye gaba: Anyi wata mummunar hatsarin shanu a jahar Legas (Hotuna)

Allah ya kiyaye gaba: Anyi wata mummunar hatsarin shanu a jahar Legas (Hotuna)

Wata babbar mota da akafi sani da suna Tirela wanda ta fito daga yankin Arewacin Najeriya makare da shanu da zata isarsu dasu kasuwannin dabbobi dake jahar Legas ta fadi a cikin Legas, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar LEGIT.com ta ruwaito lamarin ya faru ne da safiyar Alhamus 25 ga watan Oktoba, sai dai babu tabbacin abinda ya sabbaba wannan hatsari mai muni zuwa lokacin da muka tattara rahoton, amma shanu da dama sun samu munanan rauni, wasu kuma sun mutu.

KU KARANTA: An sake kwatawa: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 10 a jahar Ribas

Idan za’a tuna a shekarar 2015 ma an samu makamancin wannan hatsari akan babba hanyar Ibadan zuwa Legas, inda wata motar Tirela dauke da shanu ta yi taho mu gama da wata karamar mota, a sanadiyyar haka shanu 18 suka mutu.

Allah ya kiyaye gaba: Anyi mummunar hatsari shanu a jahar Legas (Hotuna)
Hatsarin
Asali: UGC

A wani labarin kuma wani mummunan hatsari ya faru akan babbar hanyar Ibadan zuwa Legas a ranar 23 ga watan Oktoba, inda akalla mutane tara suka rigamu gidan gaskiya a sanadiyar hatsarin.

Wannan hatsari mai muni ya faru ne a tsakanin motar marsandi da babbar motar haya Macpolo, da kuma wata motar Tirela kirar Iveco, kamar yadda shugaban hukumar kare haddura ta kasa, FRSC, reshen jahar Oyo, Clement Oladele ya bayyana.

Sai dai Mista Clement yace wanda ya aikata laifin daya sabbaba wannan hadari direban motar Macopolon, wanda shaidun gani da ido ya suka tabbatar da cewar gudun wuce raini yake yi yayin da hadarin ya faru.

“Mutane 42 hatsarin ya rutsa dasu, 34 maza, 8 takwas kuma Mata, yayin da maza uku da mata biyu suka jikkata, wasu maza bakwai da mata biyu suka mutu.” Inji Mista Clement Oladele.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng