An sake kwatawa: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 10 a jahar Ribas

An sake kwatawa: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 10 a jahar Ribas

Akalla mutane goma aka yi garkuwa dasu a yayin da wasu gungun gagga gaggan yan bindiga suka kai hari cikin karamar hukumar Akuku Toru a jahar Ribas dake yankin kudu masu kudancin Najeriya, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar LEGIT.com ta ruwaito yan bindigan sun kai harin ne da yammacin Laraba 24 ga watan Oktoba, a yayin da mutanen da aka sace suke kan hanyar dawowa daga wani gari dake makwabtaka dasu masu suna Idama, inda suka je balaguro.

KU KARANTA: Wayyo! An yi kare jini, biri jini a wata karanbatta tsakanin yan daba da Yansanda a Kano

Duk kokarin da majiyarmu ta yi na jin ta bakin shugaban karamar hukumar Akuku Toru, Rowland Sekibo ya ci tura, sakamakon lambobin wayansa basa shiga, shima kaakakin rundunar Yansandan jahar, DSP Nnamdi Omoni yace bai ka ga samun labarin ba.

Matsalar garkuwa da mutane a jahar Ribas ba sabon abu bane, inda ake yawan samun sace sace mutane musamman turawa dake aiki a kamfanonin man fetir dake garin Fatakwal, sai dai matasan yankin masu tada kayar baya ne ke aikata danyen aikin nan.

A wani labarin kuma, wasu yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mata yan tagwaye, Hassana da Hussaina dake zama a garin Dauran, cikin karamar hukumar Zurmi, a ranar Talata 23 ga watan Okotoba.

A baya dai wannan matsala kamar ta kau, musamman a lokacin da dakarun Sojojin Najeriya da sauran jami’an hukumomin tsaro suka mamaye garin suna yaki da yan bindiga, inda suka samu nasara kamawa tare da kashe wasu gagga gaggan yan bindiga da suka shahara.

Da haka sai dai iyayen wadanda aka kama ko danginsu su yi ta cinikin kudin da zasu biya yan ta’addan domin su sako musu yan uwansu, idan kuma ba haka sai su yi barazanar kashe wadanda suka kaman, musamman idan an saka Yansanda a cikin maganar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel