Masu yi don Allah: Ta sadaukar da filinta don gina Masallaci, ta bada gudunmuwar dubu 800
Wata Mata, Hajiya Fatima Muhammad ta yi namijin kokari inda ta bayar da kyautar wani katafaren filinta, tare da gudunmuwar zambar kudi naira dubu dari takwas (800,000) don gina Masallaci a wata unguwa dake jahar Sakkwato.
Jaridar Rariya ta ruwaito Hajiya Fatima ta mika wanna fili ne ga hukumar zakka da wakafi ta jahar Sakkwato ne a ranar Talata 23 ga watan Oktoba, inda tace ta sadaukar da Filin dake unguwar Guiwa layout don ginin Masallaci, ko kuma duk wani abu da zai amfanar da al’ummar Musulmai.
KU KARANTA: Yan majalisa sun kamala aiki akan sabon kudin dokokin zabe, duba muhimman dokoki 5 daga cikinsu
Majiyar LEGIT.com ta ruwaito a yayin jawabinta, Hajiya Fatima na fadin: "Na yi wannan ne lura da Hadisin Annabi S.A.W dake nuni da idan mutum ya mutu abu uku ne za su amfane shi, ciki har da wanda ya gina masallaci.
"Na zauna na yi tunanin wannan Unguwar babu masallaci, kuma shiyar ta kunshi jama'a, sai na yanke shawarar naba da wannan filin domin a yi masallai, kuma ga bohol dina nan gaban gidana a jawo a yi famfuna a yi wakafi, kuma hukuma na iya sarrfa filin zuwa duk abinda zai amfanar da al'umma". Inji ta.
Dayake jawabi a yayin karbar takardun filin, shugaban hukumar Zakkah da wakafi na jahar Sakkwato, Malam Lawal Mai Doki Sadaukin Sakkwato, ya jinjina ma kokarin da Hajiya Fatima ta yi game da wannan wakafi, inda yace itace mace ta farko da fara bayar da wakafin Fili don amfanin jama’a, haka zalika itace mace ta biyu da bayar da wakafin kudi, a cewarsa.
A jawabin nasa, Mai Doki ya bada tabbacin hukumarsa za ta yi iya bakin kokarinta don ganin ta baiwa wannan amana kulawar data dace, kuma zasu tabbatar da zasu cika sharuddan wakafi akan wanann fili kamarsu samar da shaidu, fitar da iyakan fili, da rattafa hannu.
Daga karshe Hajiya Fatima Muhammadu ta yi kira ga sauran mata da ma sauran al’umma gabaki daya dasu tabbata sun bada gudunmuwarsu wajen ciyar da addinin Musulunci gaba, da ma Musulmai gaba daya.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng