Wasu manyan tsofin 'yan ta'adda 5 da Najeriya ba za ta taba mantawa da su ba

Wasu manyan tsofin 'yan ta'adda 5 da Najeriya ba za ta taba mantawa da su ba

Tarihin Najeriya, kamar na kowacce kasa a duniya, na cike da abubuwa daban-daban, wasu na burgewa, wasu na ban dariya, wasu kuma na ban haushi.

A yau jaridar legit.ng ta kawo maku jerin wasu manyan 'yan ta'adda 5 da tarihi zai cigaba da ambaton su.

1. Lawrence Anini: An fi kiransa da "doka" wato "law" a turance, kuma ya yi fice a aiyukan ta'addanci a tsohuwar jihar Bendel a shekarun 80s.

Ya fara sana'ar tukin mota ne, daga nan kuma ya fara tuka barayi zuwa wurin fashi kafin daga bisani shi ma ya hada na shi gungun barayin.

Bayan ya yi karfi, sai ya fadada aiyukansa zuwa wasu jihohin Najeriya.

Anini ya yi fice wajen saurin kashe jami'an tsaro ko duk wanda tsautsayi ya fadawa, har ta kai ga jin sunansa na saka firgici a zukatan jama'a.

Rahotanni sun bayyana cewar hatta a taron majalisar tsaro ta shugaban kasar Najeriya a lokacin, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) sai da aka tattauna irin ta'addanci da Anini ke aikatawa.

An kama shi a ranar 3 ga watan Disamba na shekarar 1986 a birnin Benin a wani ofireshon da jami'in dan sanda, SP Kayode Uanreroro, ya jagoranta.

Wata kotun birnin Benin karkashin mai shari'a James Omo-agege ta yankewa Anini hukuncin kisa a ranar 29 ga watan Maris na shekarar 1987.

2. Dakta Ishola Oyenusi: Za a iya cewa Ishola ne dan ta'addar da ya fara yin suna a matsayin dan fashi da makami a Najeriya.

A tarihin ta'addanci a Najeriya, ana daukan Ishola a matsayin mutumin da ya kafa fashi da makami a Najeriya. Ya fara harkar fashi da makami ne bayan makamai sun shiga hannun farar hula sakamakon yakin Biyafra da aka fafata na tsawon shekaru uku, 1967 zuwa 1970.

A lokacin da yake kan ganiyar sa, Ishola ya sakawa kansa suna "Likitan fashi da kisa" saboda zai iya kashe mutum a kan karan sigari.

Fashi na karshe da ya yi kafin a kama shi, shine na kamfanin WAHUM da ke Ikeja a jihar Legas a shekarar 1971.

Babu wanda ya taba tunanin za a iya kama Ishola saboda tsananin tsafi da asirin da ya mallaka.

Jama'a da dama sun taru a bakin Bar Beach a Legas domin ganin yadda za a kashe shi.

Wani abu da ya bawa jama'a mamaki shine yadda Ishola ke murmushi duk da an daure shi za a kashe a ranar 8 ga watan Satumba na shekarar 1971.

3. Godgodo: Sunansa na gaskiya Abiodun Egunjobi kuma ido daya gare shi.

Shi ma dan fashi da makami ne amma kuma da salo irin na Anini domin ko kadan bashi da tausayi, ba ya bata lokaci wajen aika mutum lahira.

Sai da jami'an 'yan sandan jihar Legas su Ka shafe tsawon shekaru 14 kafin su kai ga kama Godgodo, hakan ya saka 'yan sanda yin biki a ranar da aka kama shi.

Dan asalin jihar Ogun, Godogodo ya yi suna saboda yadda ya iya kaucewa kamun jami'an tsaro bayan kasancewa cikin wadanda su ke nema ruwa a jallo har tsawon shekaru 10.

Anyi kiyasin cewar ya kashe jami'an 'yan sanda a kalla 100 a jihar Legas.

An kama Godogodo ne a ranar 1 ga watan Agusta na shekarar 2013.

4. Derico: Sunansa na gaskiya Okwudili Ndiwe amma an fi saninsa da Derico Nwamama a cikin tarihin manyan 'yan ta'adda da su ka taba addabar Najeriya.

Tun yana da shekaru 22 a duniya, Derico ya zama tamkar sarki a tsakanin 'yan ta'addar da ke yankin kudu maso gabas a shekarar 2000.

Ya fara sata ne tun daga yankan aljihu (sane) kafin daga bisani ya zama rikakken dan fashin da sunansa ke firgita jama'a.

Derico na yin fashi ga 'yan kasuwa, bankuna da matafiya, lamarin da ta kai ga ya saka hatta gwamnan jihar Anambra na wancan lokacin, Chinwoke Mbadijinu, cikin damuwar yadda zai magance Derico.

'Yan kungiyar bijilanti ta Bakassi sun kama Derico a ranar 3 ga watan Yuli na shekarar 2001 a hanyar sa ta zuwa Onitsa daga Agbor bayan aikata wani fashi.

A ranar 9 ga watan Yuli ne su ka kawo Derico tsakiyar kasuwar Ochanja dake kan titin Onitsa inda su ka fille masa kai a bainar jama'a.

5. Kayode Williams: Williams ya kasance daya daga cikin yaran Ishola da su ka tsira.

Ya yi halin ubangidansa, domin ba ya bata lokaci wajen yin kisa.

Amma wani abun mamaki, shine yadda daga baya ya tuba, ya koma ga Allah, har ta kai ga ya zama Bishop da ke jagorantar ibada a Coci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel