Amal bin Laden ta fadi abinda Osama ya fada na karshe Amurka a daren da aka kashe shi

Amal bin Laden ta fadi abinda Osama ya fada na karshe Amurka a daren da aka kashe shi

- Amal bin Laden, matar marigayi Osama bin Laden ta yi magana, a karo na farko, yadda sojojin kasar Amurka su ka kashe mijinta

- Sojojin Amurka na musamman (SEAL) ne su ka kashe Osama a ranar 11 ga watan Mayu na shekarar 2011 a wani gidansu da ke kan tsaunin Abbottabad a kasar Pakistan

- Jin wannan motsin ne ya saka Osama tashi a frigice, "sojojin Amurka ne," ya fada yana haki

Amal bin Laden, matar marigayi Osama bin Laden ta yi magana, a karo na farko, yadda sojojin kasar Amurka su ka kashe mijinta a kan idonta.

Sojojin Amurka na musamman (SEAL) ne su ka kashe Osama a ranar 11 ga watan Mayu na shekarar 2011 a wani gidansu da ke kan tsaunin Abbottabad a kasar Pakistan.

Amal bin Laden ta fadi abinda Osama ya fada na karshe Amurka a daren da aka kashe shi
Gidan da aka kashe Osama
Asali: Twitter

Amal ta bayar da labarin yadda aka kashe Osama da tarihin gwagwarmayar sa a cikin wani littafi (The Exile: The Flight Of Osama bin Laden) da jaridar ranar Lahadi ta kasar Ingila ta wallafa sashensa.

"Da misali karfe 11:00 na daren ranar 1 ga watan Mayu, 2011, ina kwance tare da Osama yana bacci bayan mun kammala cin abinci na wanke kwanuka.

DUBA WANNAN: Shugaban kasar Kamaru mai shekaru 85 ya sake lashe zabe a karo na 7

"Muna kwance ne cikin duhu kasancewar wurin babu wutar lantarki, amma da tsakar dare sai kawai na farka firgigit bayan na ji kamar motsin mutane na tafiya.

"Jin wannan motsin ne ya saka Osama tashi a frigice, "sojojin Amurka ne," ya fada yana haki. Yana gama fadin haka sai mu ka ji wata kara, sun balle kofar dakin mu sun shigo," a cewar Amal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng