An gano gawar Jamal Khashoggi da ake zargin masarautar Saudiyya da kitsa kashe shi

An gano gawar Jamal Khashoggi da ake zargin masarautar Saudiyya da kitsa kashe shi

- An gano gawar Jamal Khashoggi a lambun gidan wani babban jakadar kasar Saudiyya a Turkiya

- Rahotanni sun ce anyi gunduwa-gunduwa da gawarsa kuma an yiwa fuskarsa mummunan rauni

- Wannan ya yi karin haske kan zargin da ake yi na cewar masarautar Saudiyya ne ta kashe shi saboda sukar ta da ya ke yi

Rahotanni da muka samu daga Sky News ya bayyana cewar an gano gawar Jamal Khashoggi, dan jaridar kasar Saudiyya da ake zargin masarautar Saudiyya na da hannu cikin bacewarsa da yi masa kissar gilla.

Wata majiya ta fada wa Sky News cewar anyi gunduwa-gunduwa da jikin dan jaridar kuma an yi masa rauni a fuskansa.

Majiyar ta kara da cewar an gano gawar Mr Khashoggi ne a wata lambu da ke gidan wani babban jakadan kasar Saudiyya mai nisan mita 500 daga ofishin jakadancin Saudiyya na kasar Turkiya inda aka yiwa Khashoggi ganin karshe.

An gano gawar dan jaridar Saudiyya, Jamal Khashoggi
An gano gawar dan jaridar Saudiyya, Jamal Khashoggi
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Wata mace ta yi karar mijinta a kotu bisa gazawarsa wajen biya mata hakin kwanciyar aure

Hakan ya yi karin haske kan zargin da ake yi na cewar mahukunta kasar Saudiyya ne suka kashe shi sannan suka nade gawansa cikin carpet sannan suka mika wa wani domin ya je a birne gawar.

A baya dai shugaban kasar Saudiyya ya bayyana cewar ba a gano gawa Mr Khashoggi ba inda ya bukaci jami'an Saudiyya su bayyana inda gawar ta ke tunda ganin karshe da aka yiwa dan jaridar shine lokacin da ya ke shiga ofishin jakadancin Saudiyya na Turkey.

Shugaban na Turkiya ya yi kira da Saudiyya da hukunta dukkan wadanda ke da hannu cikin kissar gillar da aka yiwa dan jaridar.

Da farko dai Saudiyya ta ce Mr Khashoggi ya fice daga ofishin jakadancinta ta kofar baya amma daga bisani ta canja labarin inda ta ce dan jaridar ya rasu ne sakamakon dambe da ya yi da wasu a cikin ofishin.

Mr Khashoggi dai ya dade yana sukar gwamnati Saudiyya da Sarkin Saudiyya, Mohammed bin Salman hakan yasa ya yi hijira zuwa Amurka inda ya cigaba da sukar gwamnatin a rubutunsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164