Jonathan ya gayyaci Buhari, Atiku da Obasanjo taron kaddamar da littafin sa

Jonathan ya gayyaci Buhari, Atiku da Obasanjo taron kaddamar da littafin sa

- Tsohon Shugaban kasa Jonathan zai buga wani sabon littafin sa kwanan nan

- Sunan wannan littafi da za a buga a karshen watan gobe ‘My Transition Hours’

- Tsohon Shugaban ya gayyaci Muhammadu Buhari da su Obasanjo wajen taron

Jonathan ya gayyaci Buhari da su Obasanjo taron kaddamar da littafin sa
Tsohon Shugaba Jonathan ya aikawa goron gayyatar kaddamar da littafin sa
Asali: Facebook

Labari ya zo mana cewa tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan zai buga wani littafi game da lokacin mulkin sa kwanan nan. Jonathan ya gayyaci irin su tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo zuwa wajen kaddamar da littafin.

Haka zalika Goodluck Jonathan ya gayyaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma Abokin takarar sa da za su gwabza a 2019 watau Atiku Abubakar wajen wannan taro da za a fito da littafin sa mai suna ‘My Transition Hours’

KU KARANTA: Saboda yadda Jonathan ya sallama mulki ya sa na ke kallon sa da mutunci – Buhari

Jonathan zai kaddamar da wannan littafi ne a Ranar 20 ga Watan Nuwamba wanda ya zo daidai da ranar da zai cika shekaru 61 a Duniya. Littafin zai kunshi labarin yadda ya sha kasa a zaben 2015 da kuma yadda ya mika mulki.

Tsohon Shugaban ya gayyaci manyan Kasar nan irin su tsohon Alkalin Alkalai Salihu Alfa Belgore, da Janar Theophilus Y. Danjuma wajen kaddamar da wannan littafi. Mai Girma Gwamna Seriake Dickson shi ne mai masaukin baki.

Har wa yau, Jonathan ya gayyaci tsofaffin Shugaban Kasashen Afrika Alassane Ouattara na Ivory Coast da kuma Shugaba John Dramani Mahama wanda ya rubuta masa mukaddima wajen bikin kaddamar da wani babban littafi a Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng