An kama mutane 22 da ke da hannu a rikicin Kaduna

An kama mutane 22 da ke da hannu a rikicin Kaduna

- Hukumar 'yan sandan Najeriya ta cafke wasu mutane 22 da ta ke zargin na da alaka ta kai tsaye da kisan mutane a rikicin Kaduna

- Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Jimoh Moshood, ne ya sanar da hakan yayin wata ganawa da manema labarai

- Kazalika ya mika sakon ta'aziyya ga iyalin wadanda su ka rasa 'yan uwansu sanadiyar rikicin

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta cafke wasu mutane 22 da ta ke zargin na da alaka ta kai tsaye da kisan mutane a kasuwar Magani da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Jimoh Moshood, ne ya sanar da hakan yayin wata ganawa da manema labarai yau, a Abuja.

"Mun kama mutane 22 da ke da alaka ta kai tsaye da kisan jama'a, su na ajiye wurin mu kuma su na taimakawa jami'anmu da muhimman bayanai a kan rikicin," a cewar Moshood.

An kama mutane 22 da ke da hannu a rikicin Kaduna
Jimoh Moshood
Asali: Twitter

Moshood ya kara da cewar yanzu haka zaman lafiya ya dawo tare da bayyana cewar an sako wasu manyan mutane da aka sace yayin rikicin.

DUBA WANNAN: Allah kare masifa: Tankar dakon man fetur ta fado daga gadar Odetola a Legas

Kazalika ya mika sakon ta'aziyya ga iyalin wadanda su ka rasa 'yan uwansu sanadiyar rikicin.

"Shugaban rundunar 'yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, ya yi Alla-wadai da afkuwar rikicin. Sannan ya kafa wani kwamitin bincike na musamman da zai gudanar da bincike a kan kisan jama'ar da ba su aikata laifin komai ba," kamar yadda Moshood ya fada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel