Duk inda Obasanjo ya bi damu, ya zama wajibi mu bi shi sau da kafa – Gumi

Duk inda Obasanjo ya bi damu, ya zama wajibi mu bi shi sau da kafa – Gumi

Shahararren malamin addinin nan dake garin Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya bayyana cewa wajibi ne ga yan Najeriya da su bi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo zuwa duk inda ya karkata, inji rahoton jaridar The Cable.

Majiyar LEGIT.com ta ruwaito Gumi ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tambayoyi daga yan jarida, inda yace bai damu da duk soke soken da ake yi masa game da ziyarar sulhun da ya kai gidan Obasanjo ba, don kuwa ya san yan siyasa ne kawai suke daukan nauyin wasu mutane suna yi masa batanci a kafafen sadarwar zamani.

KU KARANTA: An fallasa kullin da gwamnonin APC 15 ke yi don ganin sun kawar da Oshiomole

Malamin ya kara da cewa a lokacin da aka gayyace shi bai yi shawara ba, don kuwa ya san sulhu alheri ne a Musulunce, inda ya kara da cewa Atiku da Obasanjo manyan mutane ne, wadanda suka dade basa ga maciji da juna, don haka yayi farin cikin shiga tsakaninsu da yayi.

Duk inda Obasanjo ya bi damu, ya zama wajibi mu bi shi sau da kafa – Gumi
Atiku Gumi
Asali: Depositphotos

Sai dai da aka tambaye shi mai yasa bai sulhu a jihohin Zamfara, Birnin Gwari, Filato da kudancin Kaduna ba, sai Gumi yace idan ana rikici irin wannan, sai an fara aika jami’an tsaro su kwantar da tarzoma, daga nan kuma sai a fara aikin sulhunta bangarorin, amma babu wanda ya taba gayyatarsa.

Bugu da kari Gumi ya bayyana cewa masu sukarsa ma sune suke ingiza wutar rikicin da ake samu a ksar nan, inda yace “Kalli gwamnan Kano da aka kama yana zuba daloli a aljihunsa, duka haka suke banda kila mutum daya ko biyu, kuma a haka wai suke yaki da rashawa.

“Tunda Atiku mutum ne mai zaman sulhu, zan goyi bayansa, amma tunda su basu son sulhu, ba zan goyi bayansu ba, ka duba misalin Kanal Sambo Dasuki, ace har yanzu basu sake shi ba duk cewa kotuna sun bada umarnin a sako shi, wai suna fakewa ne da sakinsa barazana ne ga tsaro.” Inji shi.

Hakazalika Gumi yayi kaca kaca da gwamnatin shugaba Buhari, inda yace a karkashin ikonsa Najeriya ta zama tamkar kwale kwalen dake nutsewa kuma babu abinda za’a iya yi akai. Kaga kamar Obasanjo ne, a lokacin da yaga Jonathan na karkacewa sai ya janye goyon bayansa.

“Haka ma yanzu, Buhari lalata kasar yake yi, don haka Obasanjo ya janye goyon bayan da ya bashi a baya, don haka duk lokacin da Obasanjo ya yanke shawara, ya zama wajibi a garemu mu bi shi don mu ceto kasar daga turbar tabarbarewa.” Inji shi.

Shehin Malamin yayi kira ga jama’a dasu zabi wanda suke so a 2019, amma yayi nuni da ya kamata a zabi sabon jini, amma tunda dai ba’a samu sabon jinin ba, toh sai su zabi Atiku tunda bai kai Buhari lalacewa ba, kuma zai iya farfado da tattalin arzikin kasa.

Daga karshe da aka tambayeshi mai yasa yana sukan Buhari, amma baya taba El-Rufai, sai yace “Idan ana babbakar Giwa, wake jin kaurin bera?”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel