Talakan Arewa ya fi kowa shan tsananin wahala a Gwamnatin Buhari – Gumi

Talakan Arewa ya fi kowa shan tsananin wahala a Gwamnatin Buhari – Gumi

Kwanan nan ne mu ka samu labari cewa Bajimin Malamin nan na Fikihun addinin Musulunci watau Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ba Talakawa Arewa shawara ganin an kama hanyar zaben 2019.

Talakan Arewa ya fi kowa shan tsananin wahala a Gwamnatin Buhari – Gumi
Babu wanda ya wahala a Gwamnatin nan irin Talakan Arewa inji Gumi
Asali: Twitter

Sheikh Ahmad Gumi ya nemi Hausawa su cire keta da hassada a zuciyar su idan har su na so zaman Kasar nan tayi masu dadi. Dr. Ahmad Gumi yake cewa mutane sun zabi Shugaba Buhari ne kurum saboda ya kama Barayi a kasar nan.

Babban Malamin addinin yace wannan ne kurum dalilin da ya sa aka zabi Muhammadu Buhari a 2015 kuma sai ga shi tun da Buhari ya samu mulki babu wanda ya wahala tukuf a kaf Najeriya kamar Masoyan na sa mutanen Arewacin Kasar.

KU KARANTA: 2019: Sheikh Ahmad Gumi ya ba Musulmai shawaran wanda za su zaba

A dalilin haka ne Dr. Ahmad Gumi ya nemi jama’a su daina gina ramin mugunta su gina ramin rahama domin kuwa yace su ne su ke fadawa a ciki. Dr. Gumi ya nuna cewa Bahaushen Mutum yana da tsananin keta da hassada a ko ina.

Shehin Malamin yayi wannan magana ne lokacin da yake amsa tambayar wani ‘Dalibin sa wanda yake tambaya game da abin da ya sa babban Malamin ya ke yawan tsoma baki a cikin harkar siyasar Najeriya a alhali yana mai karatun addini.

Kwanaki dai Sheikh Ahmad Gumi yayi ta magana kan wasu batutuwa a Najeriya wanda su ka hada da zaben 2019 har ta kai ya tafi wani zaman sulhu tsakanin Atiku Abubakar da Cif Olusegun Obasanjo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel