Motoci 10 da su ka fi jirgin sama tsada, hotuna

Motoci 10 da su ka fi jirgin sama tsada, hotuna

Jama'a da dama za su yi matukar mamakin jin cewar akwai motocin hawa da su ka fi jirgin sama tsada, musamman ganin cewar jirgi ya fi girma da kawa a tsarin kira idan aka kwatanta shi da mota.

Legit.ng ta ci karo da jerin wasu motoci 10 da suka fi jirgin sama tsada.

10. Bugatti Chiron - Dalar Amurka miliyan $2.7m (miliyan N826m)

Kamfanin Bugatti ne ya kera wannan mota da ake ikirarin babu mota kamar ta a bangaren gudu da kawatawa.

Farashin motar na farawa daga dalar Amurka miliyan $2.7m zuwa dalar Amurka miliyan $3m.

Motoci 10 da su ka fi jirgin sama tsada, hotuna
Bugatti Chiron
Asali: Twitter

9. Pagani Huayra BC - Dalar Amurka miliyan $2.8m (Naira miliyan N856m)

Ita ce mota ma fi tsada da kamfanin Pagani ya taba kerawa. An fara ganin motar ne a shekarar 2016 a bikin bajakolin motoci a Geneva, kasar Switzerland.

Motoci 10 da su ka fi jirgin sama tsada, hotuna
Pagani Huayra BC
Asali: Twitter

8. Ferrari Pininfarina - Dalar Amurka miliyan $3 (Naira miliyan N918m)

An kirkiri wannan mota ne a shekarar 2013 domin tunawa da mutumin da ya fara kirkirar motocin Pininfarina.

Mutane 6 ne kacal su ka mallaki motar a duniya, kuma su ma kamfanin ne ya zabe su. Hakan ya saka ta daya daga cikin motoci ma fi karanci a duniya.

Motoci 10 da su ka fi jirgin sama tsada, hotuna
Ferrari Pininfarina
Asali: Getty Images

7. Aston Martin Valkyrie - Dalar Amurka miliyan $3.2 (Naira miliyan 979)

Har yanzu kamfanin wannan mota bai fitar da farashinta ba saboda sai shekarar 2019 za ta shiga kasuwa.

Sai dai masana motoci da farashinsu sun yi kiyasin cewar kudinta ba zai taba gaza Dalar Amurka miliyan $3.2 ba.

Motoci 10 da su ka fi jirgin sama tsada, hotuna
Aston Martin Valkyrie
Asali: Twitter

6. Bugatti Veyron - Dalar Amurka miliyan $3.4 (Naira biliyan N1.04bn)

Mota ce kirar kasar Jamus da aka canjawa fasali da fasaha har sau hudu tun bayan shigowar ta kasuwa a shekarar 2005. Ta na cikin motoci masu masifar gudu a duniya.

Motoci 10 da su ka fi jirgin sama tsada, hotuna
Bugatti Veyron
Asali: Twitter

5. Lykan Hypersport - Dalar Amurka miliyan $3.4 (Naira biliyan N1.04)

Daya daga cikin dalilin tsadar wannan mota shine na cewar an yi fuskar fitilar ta ne da gwal. Kamfanin W motors da ke kasar Lebanon, a yankin Larabawa, ya fara kera motar.

Motoci 10 da su ka fi jirgin sama tsada, hotuna
Lykan Hypersport
Asali: Twitter

4. McLaren P1 LM - Dalar Amurka miliyan $3.6m (Naira biliyan N1.1)

Ita dama an kera ta ne domin wasu tsirarun masu saya daga kasashen Amurka, Japan, Ingila da Daular larabawa. Injina biyu gare ta, kowanne na da fulogi 8. An kewaye injinanta da zinare.

Motoci 10 da su ka fi jirgin sama tsada, hotuna
McLaren P1 LM
Asali: Twitter

3. Lamborghini Veneno Roadster - Dalar Amurka miliyan $4.5m (Naira biliyan N1.38bn)

Kalmar Veneno na nufin guba ko dafi a Hausa. Kamfanin lamborghini ya kirkiri wannan mota ne domin murnar cika shekaru 50. Motar na tafiyar mayil 60 a sa'a daya cikin dakika 2.9 kacal.

Motoci 10 da su ka fi jirgin sama tsada, hotuna
Lamborghini Veneno Roadster
Asali: Twitter

2. Koenigsegg CCXR Trevita - Dalar Amurka miliyan $4.8m (Naira biliyan N1.47bn)

Ita ce mota ma fi tsada da ta fara samun damar taka kan titi da izinin kamfanin kera motoci na duniya. Jikinta na zallar gwal ne.

Motoci 10 da su ka fi jirgin sama tsada, hotuna
Koenigsegg CCXR Trevita
Asali: Getty Images

1. Sweptail Rolls Royce - Dalar Amurka miliyan $13m (Naira biliyan N3.99bn)

Kafin ka kasa rufe baki saboda mamakin tsadar wannan mota, ya kamata ku sani cewar kamfanin wannan mota ya kera ne bisa tsarin da wani mutum ke so. Sai dai har yanzu kamfanin ya ki sakin bayanai a kan wannan mutum.

Motoci 10 da su ka fi jirgin sama tsada, hotuna
Sweptail Roll Royce
Asali: Twitter

Karin wani abin mamaki a kan wannan mota shine gurin zaman mutum biyu kacal ta ke da shi kuma duk kofofin jikin motar na'urori masu kwakwalwa ne a manne a jiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng