Gwamna Shettima ya sallaci gawar Hauwa Liman budurwar da Boko Haram su ka kashe, hotuna
A ranar Laaba ne wani tsagin kungiyar Boko Haram mai suna Daular Musulunci ta yankin Afrika maso yamma (ISWAP) ta kashe daya daga cikin ma’aikatan kungiyar agajin gaggawa (Red Cross) Hauwa Liman, bayan wa’adin da suka baiwa gwamnatin tarayya ya cika.
A jiya juma'a ne gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya ziyaraci jana'izar marigayiya Hauwa Liman tare da shiga sahun yi mata sallar jana'iza ba tare da gawa ba, wacce aka kira da 'Salatul Ghaib'.
Babban limamin masallacin jami'ar Maiduguri, Imam Muhammad Goni Ali Gabcha, ne ya jagoranci sallar a gidan su marigayiya Hauwa da ke unguwar Mairi a garin Maiduguri.
Jim kadan bayan da sallar, gwamna Shettima ya yiwa mahaifin marigayiya Hauwa gaisuwa tare da bayyana cewar aiyukan 'yan Boko Haram ta'addanci ne da bashi da alaka da addinin musulunci.
DUBA WANNAN: Ta baci: Gwamnatin Kaduna ta saka dokar hana fita a yankin jihar
Kazalika ya dauki alkawarin agazawa iyayenta bisa sadaukarwa da diyar su ta yi. Alhaji Muhammad Liman, mahifin marigayiya Hauwa ya godewa gwamnan bisa kulawa da damuwar da ya nuna a kan mutuwar diyar ta sa.
Hauwa Liman, dalibar Jami’ar Maiduguri ce wacce ke aiki da kungiyar Red Cross a garin Rann, jihar Borno.
Mayakan kungiyar Boko Haram sun yi garkuwa da ita tare da abokan aikinta 2 Alice Loksha Ngaddah da Saifura Husseini Ahmed a wani hari da su ka kai. Kazalika sun kashe sojoji hudu da yan sanda hudu a harin.
Mayakan na Boko Haram ba su saki gawar marigayiya Hauwa ba bayan sun kashe ta har zuwa lokacin da aka yi ma ta sallar jana'iza a jiya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Asali: Legit.ng