'Kungiyar 'Daliban Najeriya ta bai wa shugaba Buhari wa'adin Kwanaki 7 ya binciki dambarwar rashawa ta Gwamnan Jihar Kano Ganduje

'Kungiyar 'Daliban Najeriya ta bai wa shugaba Buhari wa'adin Kwanaki 7 ya binciki dambarwar rashawa ta Gwamnan Jihar Kano Ganduje

'Kungiyar dalibai ta Najeriya NANS, National Association of Nigerian Students, a yau Juma'a ta bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wa'adin kwanaki bakwai akan ya tabbatar da gaskiya kan zargin aikata rashawa ta gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, kungiyar ta baiwa shugaba Buhari wa'adin mako guda a kan ya tabbatar da sahihanci shahararren faifan bidiyon da ya bayyana da ke nuna gwamnan jihar Kano na amsar cin hanci daga wurin wani dan kwangila.

Kungiyar ta sha alwashin kunyata shugaba Buhari a idon duniya wajen hada gangami na dalibai da kuma matasa domin aiwatar da zanga-zanga a fadin kasar nan muddin ya gaza tunkarar lamarin cikin gaggawa.

'Kungiyar 'Daliban Najeriya ta bai wa shugaba Buhari wa'adin Kwanaki 7 ya bincike dambarwar rashawa ta Gwamnan Jihar Kano Ganduje
'Kungiyar 'Daliban Najeriya ta bai wa shugaba Buhari wa'adin Kwanaki 7 ya bincike dambarwar rashawa ta Gwamnan Jihar Kano Ganduje
Asali: UGC

A yayin haka kungiyar ta barrantar da kanta kan rahoton wata kungiya da ta aiwatar da zanga-zangar rashin amincewa da wannan lamari a jihar Kano.

KARANTA KUMA: Ambaliyar Ruwa: Mataimakin Shugaban Kasa ya kai ziyarar jajantawa jihar Bayelsa

Cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a birnin Abeokuta na jihar Ogun, kungiyar ta bayyana haka ne da sanadin kakakin ta na kasa, Adeyemi Amoo, da ya nemi shugaba Buhari akan ya gaggauta tabbatarwa da al'ummar kasar nan akidarsa ta gaskiya da yakar rashawa.

Kazalika kungiyar ta kuma sha alwashin kaddamar da shugaba Buhari a matsayin ma'abocin rashawa muddin ya gaza kafa kwamitin amintattu da za su gudanar da bincike akan gwamnan jihar Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel