Babban magana: Wani matashi ya nufi Abuja a kasa daga Sakkwato don mara ma Atiku baya

Babban magana: Wani matashi ya nufi Abuja a kasa daga Sakkwato don mara ma Atiku baya

Wani matashi mai suna Ibrahim Watatsiya zai ya nufi babban birnin tarayya Abuja a kasa tun daga jahar Sakkwato birnin Shehu yana tattaki don bayyana goyon bayansa gad an takarar shugaban kasa Atiku Abubakar, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Sai dai majiyar LEGIT.com ta ruwaito a yanzu haka ana sa Ibrahim sarkin tafiya zai shiga babban birnin tarayya Abuja, kamala tafiyar kilomita dari shida da tamanin (680km) a kasa.

KU KARANTA: Labari mai dadi: Kasar Amurka ta kulla yarjejeniyar dala miliyan 10 da jahar Kebbi don inganta noma

Watatsiya mai shekaru 29 ya bayyana ma majiyarmu cewa ya fara wannan tattaki ne tun a ranar 7 ga watan Oktoba, kimanin awanni kadan kenan bayan an bayyana tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP.

Bincike a tsawirar shafin Google ya nuna nisan dake tsakanin jahar Sakkwato da Abuja ya kai kilomita dari shida da tamanin (680km), kuma sai an kwashe awa tara da mintuna goma sha biyar (9hr 15min) za’a isa Abuja daga Sakkwato a mota.

A jawabinsa ga manema labaru a yayin da ya isa jahar Kaduna, Watatsiya yace yana sana’ar saye da siyarwa ne na wayar hannu, kuma yace burinsa na shiga wannan tattaki shine don haduwa da Atiku ido da ido tare da bayyana masa cewa maatsan Najeriya na goyon bayansa dari bisa dari.

“Jim kadan bayan an sanar da Atiku ya lashe zaben fidda gwani na yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ne na kamo hanya, a yanzu haka ina Rijana, ina fatan zan shiga Abuja a ranar Asabar, ko kuma da Lahadi da sassafe.

“Na ratsa garuruwa daban daban daga Sakkwato, wasu daga ciki sun hada da Imasa, Talatar mafara, Tumfafiya, Mayanci, Bungudu, Gusau, Lalan, Kwatarkwash, Tsafe da Kuchere.” Inji shi.

Daga karshe ya bayyana cewa a yan kilomita daya rage masa shiga Abuja, yace ya kosa ya isar ma gwanin nasa Atiku Abubakar shine ya cigaba da samawa ma matasa ayyukan yi kamar yadda ya saba. “Wannan shine dalilin zuwana Abuja.” Inji shi

Ku biyo mu a https://facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng